Shahararren dan kwallon Brazil kuma tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen da Manchester City na Ingila Robinho ya fara yunkurin sake komawa Ingila don cigaba da kwallo.
Robinho dan kimanin shekara 32, a shekarar 2010 ce ya bar kulob din Manchester City ya koma Brazil daga baya kuma ya sake komawa Chaina don yin kwallo.
A kakar wasan da ta wuce ne kwantaraginsa ta kare da kulob din Ghangzhou Ebergrande na Chaina al’amarin da ya sa yanzu ya kasance dan kwallo mai cin gashin kansa.
Jaridar Daily Mail ta Ingila ta kalato cewa tuni wakilan dan kwallon suka tattauna da mahukunta kulob din Swansea City da kuma na Leicester City na Ingila a game da yiwuwar komawarsa daya daga cikin kulob din.
“Dukkan kulob din biyu suna bukatar karfafa ’yan kwallon gabansu, don haka akwai yiwuwar su dauki Robinho duk da an rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo ganin dan kwallon ba shi da kwantaragi da kowane kulob a halin yanzu, don haka yana da damar canza sheka a duk lokacin da ya ga dama,” inji wata majiya.
Robinho wanda ya yi suna a fagen kwallo a shekarun baya, tauraruwarsa ta yi kasa ne tun bayan da ya bar Ingila ya koma Chaina don ci gaba da kwallo a shekarar 2010. Yanzu bayan kwantaraginsa da kulob din Chaina ta kare ne yake son sake komawa Ingila don ya cigaba da kwallo a gasar rukunin firimiya da ta fi yin fice a daukacin duniya.
Robinho ya fara yunkurin komawa Ingila
Shahararren dan kwallon Brazil kuma tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen da Manchester City na Ingila Robinho ya fara yunkurin sake komawa…