✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Roberto Carlos zai kawo ziyara Najeriya

Ana sa ran tsohon dan kwallon Brazil da Real Madrid na Sifen Roberto Carlos zai kawo ziyara Najeriya. Zai kawo ziyarar ce a ranar 18…

Ana sa ran tsohon dan kwallon Brazil da Real Madrid na Sifen Roberto Carlos zai kawo ziyara Najeriya.

Zai kawo ziyarar ce a ranar 18 ga watan nan da muke ciki don bude sansanin horar da matasa kwallo wanda kulob din Madrid zai bude a Najeriya.

Bayanin da kulob din ya fitar a yanar sadarwarsa an nuna Roberto Carlos zai shigo Najeriya ne tare da Inigo ballejo (Jakadar kulob din Madrid mai kula da Nahiyar Afirka da kuma Gabas ta Taskiya) don halartar bikin bude cibiyar horar da matasa kwallo a Najeriya wato Real Madrid Foundation Clinic Nigeria.

Yomi Umar, Daraktan Kamfanin SPR da suka shirya bikin a Najeriyua ya ce makasudin bude cibiyar Madrid a Najeriya shi ne don a rika zakulo matasan ’yan kwallo don amfanin kulob din da wasu.   Hasalima za a iya daukar wadanda suka fi nuna kwazo zuwa kulob din Madrid na matasa da ke Sifen don a ci gaba da ba su horo.

Ya ce Roberto Carlos da shi ma Jakadan kulob din Madrid ne, ana sa ran zai gabatar da jawabi a game da karfafa wa matasa gwiwa a kan kwallon kafa.

A ranar 17 ga watan Fabrairun 2018 ne ake sa ran Cibiyar za ta tattaro matasa daga kowane bangare na Najeriya don a horar da su kwallon kafa a karkashin shahararrun masu horarwa.

Daga nan ne za a ci gaba da sanya ido a kan matasan da aka horar don ganin sun ci gaba da samun daukaka, inji Yomi Umar.