✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Roberto Carlos ya samu karuwa ta 9

 Tsohon dan kwallon Brazil da kulob din Real Madrid na Sifen Roberto Carlos a ranar Lahadin da ta wuce ne ya bayar da sanarwar matarsa…

 Tsohon dan kwallon Brazil da kulob din Real Madrid na Sifen Roberto Carlos a ranar Lahadin da ta wuce ne ya bayar da sanarwar matarsa mai suna Marina ta haifar masa ’ya da hakan ta sa kawo yanzu yake da ’ya’ya 9 a tsakanin mata biyu da ya aura.

Kawo yanzu Marina dai ita ce matarsa  kuma ta haifar masa ’ya’ya biyu ne tun lokacin da suka yi aure.  Ita daya matar da suka rabu da dadewa ta haifar masa ’ya’ya bakwai ne da hakan ta sa dan kwallon yake da ’ya’ya tara a tsakanin mata biyu.

A ranar Lahadi ne aka ruwaito dan kwallon ya sanar da labarin haihuwar da aka yi masa  a shafin sadarwarsa na Instagram.

Dan kimanin shekara 44, Roberto Carlos ya yi suna a fagen kwallo musamman a kasarsa Brazil da kuma a kulob din Real Madrid.

Ya yi wa kulob da dama kwallo ciki har da Inter Milan na Italiya da Real Madrid na Sifen da Fenerbahce na Turkiyya da kuma Delhi Dynamos da ke Indiya.  A shekarar 2015 ne ya daina kwallo bayan ya yi ritaya a kulob din Dynamos na Indiya inda ya koma Brazil ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.