Mukaddashin Shugaban Riki na Jami’ar Legas (UNILAG) Farfesa Omololu Soyombo ya sauka daga mukamin bayan Gwamnatin Tarayya ta sa baki a rikicin shugabancin jami’ar.
Soyombo ya sauka ne “nan take” a ranar Asabar, bayan Gwamnatin Tarayya ta umarci Majalisar Jami’ar da ta mika sunan wanda za ta nada a mukamin.
“A ranar Juma’a 21 ga Agusta 2020 mun samu labarin Gwamnatin Tarayya ta nada Kwamiti na Musamman da zai Ziyarci Jami’ar Legas, ta kuma umarci Majalisar Jami’ar ta mika mata sunan wanda za a nada Mukaddashin Shugaban Jamai’a. Saboda haka na ajiye mukamin nan take a matsayin Mukaddashin Shugaban Jamia’r”, inji sanarwar.
Majalisar Gudanarwar UNILAG karkashin jagorancin Dakta Wale Babalakin ne ya nada Farfesa Soyombo bayan sauke Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, bisa zargin sakaci da aiki da kuma almundahana.
An yi ta kai-komo kan lamarin wanda Farfesa Ogundipe da wani bangare na jami’ar suka ce haramtacce ne suka kuma zargi Dakta Babalakin da neman haddasa fitina a jami’ar.
Da yake sanar da saukarsa, Farfesa Soyombo ya bukaci al’ummar jami’ar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana da bin doka.
“Ina godiya matuka ga ma’aikata da daliba da kungiyoyin ma’aikata da tsoffin dalibai da daukacin al’umma bisa gagarumar goyon bayan da suka ba ni a cikin kwana 10 da suka gabata da aka nada ni Mukaddashin Shugaban Jamai’ar a ranar 12 ga watan Agusta, 202”, inji shi.