Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bukaci ganawa da Shugaban Rasha, Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelenskyy kan rikicin kasashen masu makwabtaka da juna.
Guterres na son ganawa da shugabannin a kasashensu ne a yayin da rikicin da ya barke a tsakaninsu a watan Fabrairu ke kara lakume rayuka da dukiyoyi.
“Sakatare-Janar ya ce a wannan hali mai matukar hadari, zai so ya tattauna matakan gaggawa na samar da zaman lafiya a Ukraine da kuma makomar ra’ayin bangarori daban-daban bisa kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa,” in ji Kakakin Majalisar, Stéphane Dujarric.
Sanarwar na zuwa ne washegarin da Guterres ya bukaci a dakatar da ayyukan jin kai a Ukraine gabanin bikin Ista a karshen makon jiya.
Dujarric, ta ce tuni aka ba wa wakilan kasashen biyu takardar neman tattaunawar ta Guterres, wanda ke son ganawa da Putin a birnin Moscow, da kuma Mista Zelenskyy a Kiev.
“Ya jaddada cewa Ukraine da Rasha na daga cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya kuma da aka kafa ta da su,” a cewar Dujarric.