✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine: Farashin gangar danyen mai zai iya kai wa $300 – Rasha

Rasha dai ita ke samar da sama da kaso 40 cikin 100 na iskar gas din da ake amfani da ita a Turai.

Kasar Rasha ta gargadi kasashen Yamma da cewa farashin danyen mai na iya kai wa kusan Dalar Amurka 300 kan kowacce ganga a kasuwannin duniya muddin suka hana ta fitar da nata man.

Rasha dai ita ke samar da sama da kaso 40 cikin 100 na iskar gas din da ake amfani da ita a Turai.

A wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin din kasar ranar Litinin, Mataimakin Fira-ministan kasar, Alexander Novak, ya yi gargadin cewa tabbas duniya za ta dandana kudarta muddin aka dauki matakin hana kasarsa fitar da man ta, da kuma rufe babban bututun da ke aike wa Jamus iskar gas daga Rashan.

Ya ce, “Karin farashin da za a samu a duniya hankali ba zai dauka ba. Zai iya kai wa $300 kan kowacce ganga, in ma bai haura hakan ba.”

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da kawayenta ke barazanar daina sayen man kasar Rasha kwata-kwata, kan matakin da ta dauka na mamaye Ukraine.

Tuni dai Shugaban Amurka Joe Biden ya fara fuskantar matsin lamba daga ’yan majalisar kasar kan ya datse duk wata huldar cinikayya da Rasha, ciki kuwa har da ta danyen man, ko da yake har yanzu bai yanke shawara kan matakin da zai dauka a kai ba.

Kasashen Yamma dai na ci gaba da kakaba wa Rashar takunkumi iri-iri kan matakin nata a Ukraine.

Rasha dai ita ce kasar da ta fi fitar da danyen mai a fadin duniya, inda take fitar da kusan ganga miliyan bakwai a kullum, kwatankwacin kaso bakwai cikin 100 na man da ake bukata a duniya.

Ko a ranar Litinin din nan, an ce farashin man ya doshi Dala 140 kan kowace ganga, farashi mafi girma tun shekarar 2008.