Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar fargaba a game da yadda rikicin Sudan ke kokarin rikidewa zuwa na kabilanci.
A cewar hukumar, lamarin ya fi kamari ne a lardin Darfour, kuma hakan na tilasta wa fararen hula tserewa daga yankin.
- Dan Brazil ya ba da wasiyyar kyautar da dukiyarsa ga Neymar idan ya mutu
- Tattalin arzikin Najeriya zai habbaka a bana, in ji Bankin Duniya
Alkaluman Majalisar na nuni da cewa sama da mutane dubu 560 da suka bar Sudan ne ke rayuwa a Chadi.
Christophe Garnier, jagoran ayyukan gaggawa a kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres a garin Adré da ke kasar Chadi, ya bayyana halin da ake ciki yanzu haka inda yake cewa: “Lalle babban iftila’i ne da ke fuskantar ayyukan jinkai, hakazalika halin da ake ciki na da matukar tada hankali, saboda hatta yadda ake samun kwararar dubban ’yan gudun hijira zuwa garin Adre, abu ne da ya yi matukar zo wa jama’a a yanayi na ba zata. Alkaluman da ake samu daga ko’ina, na kara tabbatar da cewa sam babu sauki a lamarin, musamman yanayin da wadannan mutane ke rayuwa a nan Adre, gaskiya akwai tausayi.
“Akwai karancin abinci, ba kowa ke samun damar isa ga cibiyoyin kiwon lafiya ba, a zancen da muke yi yanzu haka akwai barazanar barkewar cututtuka irinsu kyanda da amai da gudawa a cikin sansanonin ’yan gudun hijira,” in ji jami’in.
Ya kuma kara da cewa, akwai dimbin ’yan gudun hijira da ke rayuwa a filin Allah, ba dakuna, ba tanti, haka su ke rayuwa a fili ba komai.
Sai dai ya ce kungiyoyin agaji da suka hada da MSF da kuma Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ne ke iya kokarinsu domin taimaka wa mutanen da kuma tsugunar da su cikin sansanoni.
“Amma tabbas akwai manyan kalubale a gabanmu,” a cewarsa. (RFI)