✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sudan: Abu 7 da aka cimma yarjejeniya a kansu

Sai dai ba cimma matsaya ta karshe ba kan rikicin ba a tattauanwar da kasashen Saudiyya da Amurka suka shiga tsakani ba

Bangarorin da ke yaki da juna a kasar Sudan sun kulla wata yarjejeniya da nufin kare fararen hula a rikicin.

Sai dai ba cimma matsaya ta karshe ba kan rikicin ba a tattauanwar da kasashen Saudiyya da Amurka suka shiga tsakanin sojojin Sudan da dakarun gaggawa na RSF.

Don haka za a ci gaba da nufin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na kusan kwanaki 10 don saukaka ayyukan jin kai da isar da kayayyakin jin kai cikin aminci da kuma janye sojoji daga asibitoci.

Haka nan za a ci gaba da tattaunawar don kawo karshen tashin hankalin gaban daya.

Ga abubuwa bakwai da da ke  kunshe cikin yarjejeniyar ta ranar Alhamis  a birnin Jiddah, da nufin kuma kare rayukan fararen hula da ayyukan jinkai.

1. Fifita baar da kariya da jin dadin fararen hula hula a yaushe tare da ba su damar wucewa cikin amince a yankunan da fadan ya shafa.

2. Mutunta hakkokin dan Adam da dokokin kasa kasa da kasa da suka wajabta banbance tsakanin fararen hula da sojoji, da rashin amfani da farar hula a matsayin garkuwa, da mutunta cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu.

3. Bari a ci gaba da manyan ayyukan jin kai ba tare da hana musu ruwa gudu ba da kuma tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar ma’aikatan agaji da kare ma’aikatan jin kai da rashin tsoma baki a ayyukansu.

4. Alkawarin kaare mutunta dokokin jin kai na duniya.

5. Ba da damar masu aikin da suka dace, don daukar duk matakan da ake bukata don binne matattu tare da hadn gwiwar hukumomin da abin ya shafa.

6. Tabbatar da cewa duk mutanen da ke aiki a karƙashin umarnin sojojin da RSF sun bi dokar ba da agaji ta duniya.

7. Bada fifikon tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na gajeren lokaci domin saukaka isar da agajin gaggawa da dawowar muhimman ayyuka da kuma fadada tattaunawa domin kawo karshen rikicin.

Fadan da aka fara a watan jiya tsakanin Babban Hafsan Sojin kasar, Janar  Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar RSF, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 750.

Rikicin da aka fara a ranar 15 ga watan Afrilu ya kuma sanya dubban daruruwan mutane tserewa daga gidajensu, inda adadin mutanen da ke gudun hijira a Sudan ya ninka fiye da ninki biyu cikin mako guda, ya haura 700,000, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa karin mutane miliyan biyar za su bukaci agajin gaggawa a cikin kasar Sudan, wasu dubu 860 kuma za su yi gudun hijira zuwa makwabtan kasashe da ke fama da rikici a daidai lokacin da kasashe masu arziki suka janye tallafi.