✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin siyasa: Hadin kan malaman addinai shi ne mafita

Wani malamin jami’a, Dakta Isiaka Mustapha ya yi kira ga shugabannin addinai da su hada kai domin kawo karshen rikice-rikicen siyasa a Najeriya. Da yake…

Wani malamin jami’a, Dakta Isiaka Mustapha ya yi kira ga shugabannin addinai da su hada kai domin kawo karshen rikice-rikicen siyasa a Najeriya.

Da yake jawabi a taron laccar da aka shirya kan gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo cikin lumana, Dakta Mustapha, ya koka cewa shugabannin addinai sun gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na gina al’umma, wanda ya haddasa matsaloli da dama.

“Ba za iya magance matsalar dabar siyasa ba, sai dole malaman Musuluncin sun hadu da takwarorinsu na Kiritsa, kafin su san yadda za su bullo wa matsalar.

“Idan ba haka ba to da wuya a iya magance matsalar saboda manyan ’yan sun fara amfani da matsalar suna hana gudanar da zabe cikin lumana da cigaban kasa”, inji shi.

Malamin da da ke koyarwa a Sashen Gudanar da Mulki na Jamai’ar Benin, ya ce gazawar ta shugabannin addinai ta sa harkar siyasar ta koma ta kudi da dabanci da karairayi fs cin amanar kasa da kuma nuna bambancin kabilanci da addini.

A jawabinsa ga taron da Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta shirya a garin Benin, malamin jami’an ya ce abun kunya ne yadda malaman addini suka koma suna amsar kudi daga hannun ’yan siyasa.

Ya kara da cewa talauci da rashin aikin yi sun sa matasa sun koma abin amfanin ’yan siyasa wajen tayar da zaune tsaye

A cewarsa, tunanin samun kudai ba tare da wahala ba da ke tattare da siyasar kasar shi ne ya kawo karuwar rikice-rikicen siyasa.

Aminiya ta ruwaito cewa taken taron shi ne, gudunmuwar gwamnati da hukumomin da ba na gwamanti ba wajen kawar da rikicin siyasa.