✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Rikicin Rasha da Ukraine zai kawo tsadar burodi a Najeriya’

Rasha dai ita ce kasar da ta fi noma alkama a duniya.

Akwai yiwuwar rikicin da ake fama da shi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine ya sa farashin burodi ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya.

Burodi dai na daya daga cikin abincin da aka fi amfani da su a gidajen ’yan Najeriya da dama; ba talaka ba mai kudi.

Rasha dai ita ce kasar da ta fi kowace kasa fitar da alkama a duniya, inda take samar da sama da kaso 18 cikin 100 na alkamar da ake amfani da ita a duniya.

Hakan dai na nufin muddin yakin ya shafi samar da alkamar a kasar, akwai yiwuwar farashinta ya karu a kasuwannin duniya, ciki har da na Najeriya, lamarin da ka iya haifar da karin kudin duk wani dangin abincin da ake sarrafawa daga alkamar.

A tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 dai, farashin burodi ya karu da sama da kaso 80 cikin 100 a Najeriya.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce alkama ita ce abinci na uku da aka fi amfani da shi a kasar, yayin da kasar ke iya noma kaso daya cikin 100 kacal nata, ake shigo da akasarinta kuma daga ketare.

Hakan dai ya sa Najeriya kashe sama da Dalar Amurka biliyan biyu a kowace shekara wajen shigo da alkama daga kasashen waje.

A shekarar 2019 kadai, Rasha da Ukraine sun samar da daya bisa hudu na alkamar da aka yi amfani da ita a fadin duniya, kamar yadda Cibiyar sa ido kan Harkokin Tattalin Arziki (OEC) ta tabbatar.

Tuni dai Kungiyar Masu Gasa Burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce babu makawa yanayin zai kara farashin burodin a Najeriya kowane lokaci daga yanzu.