Rikicin da ke ruruwa a tsakanin Rasha da Ukaren ya mamaye kafafen yada labarai da majalisun al’umma kama daga na Turai zuwa sauran nahiyoyin duniya.
Tuni dai masana ke ta yin fashi baki a kan abubuwan da suka haddasa rikicin, da bangarorin da abin ya shafa, da kuma kalubalen da za a fuskanta.
Sai dai wasu masu fashin bakin sun alakanta rikicin da kabilanci, da kuma neman bijire wa Rasha da gwamnati mai mulki a Ukraine ta yi, lamarin da ya saba wa tsohuwar alakar da ke tsakaninsu.
Kamar yadda tarihi ya nuna, a da kasashen Ukraine da Rasha a hade suke a karkashin tsohuwar Tarayyar Soviet (Soviet Union) amma daga bisani Ukraine ta samu ‘yancin kai a shekarar 1989 sakamokon wargajewar Tarayyar.
A yanzu, ita kasar Ukraine ta fara kulla kawance da kasashen Yamma, tare kuma da neman zama mamba a Kungiyar Tsaro ta NATO, lamarin da bai yi wa Rasha dadi ba.
Kamar yadda tarihi ya nuna, Tarayyar ta Soviet ta yi nasarar bunkasa tattalin arzikin kasar Ukraine a lokacin tana karkashin ta, kuma kasar ta kasance iyaka tsakanin kasar Rasha da kasashen Tarayyar Turai.
Me ya haddasa rikicin?
Kamar yadda masu fashin baki suka zayyana, a duk lokacin da ka ji kasashen duniya sun yi tsuwwa, da ka bincika za ka tarar suna yin hakan ne domin kare martaba ko wata bukatar kasashensu.
Ita dai kasar Rasha, kamar yadda masana suka bayyana, tana matsa wa Ukraine lamba ne don ganin cewa ba ta ci gaba da zama mamba a NATO ba.
Haka kuma Rasha tana fafutukar ganin cewa kungiyar ta NATO da kasar Amurka sun jaye dakarunsu da kayan yakinsu daga Ukraine.
Volodymyr Zelenskyy
A bangaren Ukraine, Shugaban kasar, Volodymyr Zelenskyy, ya ce ba zai yi wa abubuwan da suka jibanci martabar kasarsa rikon sakainar kashi ba.
Bai yarda wata kasa ta tsoma baki a al’ammuran huldar kasarsa da kasashen waje ba.
Ya kuma ce Ukraine ba za ta yi zaman tattaunawa kai tsaye ba da ‘yan tawayen kasar masu goyon bayan Rasha.
Wadannan sharudda da Ukraine da gindaya suna cikin abubuwan da suka harzuka Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya dauki matakin girke sojoji 100,000 da makamai bila adadin a iyakarsa da kasar Ukraine.
Ko da dai wasu masana na ganin cewar Shugaba Putin ya tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro, amma wasu sun fi karkata ga cewar ya hassala ne ganin akwai rainin hankali, duba da cewar tsasonsu daya da kasar Ukraine ta fuskar al’adu da harshe, musamman ta gabashin kasar.
Rikicin kabilanci
Wani mai fashin baki, kuma tsohon kadan Najeriya a kasashen Pakistan da Afghanistan, Dauda Danladi, ya ce mutane ba za su fahimci sarkarkiyar takaddamar ba har sun san cewar rikicin kabilanci ne.
“Kada mu dauka wai a kasashen Afirka kawai ake rikicin kabilanci; wani abu ne da ya game duniya.
“Ukraine ta samu ‘yancin kai ne a shekarar 1989, amma har yanzu yare da al’adu sun hada su.
“Mafi yawan mazauna gabashin Ukraine da harshen Rasha suke magana, kuma ita kasar ta yi iyaka da nahiyar Turai saboda haka take da matukar muhimmanci ga kasar Rasha.
“Duba da siyasar duniya a yau da kowacce kasa take neman fadada siyasarta, Rasha na da bukatar fadada guraren da karfin sojinta da siyarsarta za su kai, kuma Ukraine na ciki.
“Ku tuna, ko lokacin da kasar ta Ukraine ta samu ‘yancin kai, akwai jam’iyyu masu ra’ayoyi kashi uku da suka fafata a zabe, amma masu ra’ayin Rasha suka fara mulkin kasa.
“Akwai jam’iyyu masu ra’ayin Rasha, akwai jam’iyyu masu ra’ayin kasashen Yamma, akwai kuma ‘yan kishin kasa.
“To a yanzu jam’iyya mai ra’ayin kasashen Turawan Yamma ke mulki, hakan ya sa Ukraine ta zama mamba a kungiyar NATO, lamari da bai yi wa Rasha dadi ba.
“Haka nan kuma a ka’ida, idan Rasha ta kai wa Ukraine hari dole ne kungiyar NATO ta kare ta.
“Kuma wannan shi ke sa ake kai ruwa rana a tsakanin Rasha da NATO da kasar Amurka.
“Ya kamata a sani, kai farmakin da Rasha za ta yi a kasar Ukraine tamkar kai wa kasashen Turai farmaki ne, wanda ko shakka babu zai wanzar da Yakin Duniya na Uku”, inji Ambasada Danladi.
Teburin sulhu
Ya kuma ce bisa la’akari da hakan ne ya yi hasashen cewar zai yi wahala Rasha ta kai wannan farmakin.
“Za su zauna ne a teburin shawara, kuma kowa ya yi hakuri da abin da ya samu”, inji tsohon jami’in na diflomasiyya.
Daga karshe, mun ga yadda kasashen duniya da suka hada da Amurka da Isira’ila da Ingila da Jamus da Belgium da Italiya da Japan da dai sauransu suka kwashe jakadunsu daga Ukraine tare kuma da bayar da shawara ga ‘yan kasarsu mazauna can da su yi kaura.
Amurka kuma ta janye sojoji 150 da ke horar da sojojin kasar ta Ukraine.
Sai dai Rasha ta ce ba ta da niyar kai wa Ukraine hari kuma ta fara janye sojojinta daga yankin, amma NATO da Amurka sun karyata hakan.