A halin yanzu dai an yi ittifakin cewar yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine shi ne mafi girma da muni da aka gani a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu, inda wata kasa ta afkawa wata.
Kamar yadda Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito sa’o’i kalilan bayan yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, gwamnatin Rashan ta sanar da lalata cibiyoyin sojin Ukraine sama da 70, ciki har da filayen saukar jiragen sama 11.
- Ukraine ta nemi kasashen duniya su dauki mataki kan mamayar Rasha
- Jama’a na neman mafaka a Ukraine saboda firgici bayan mamayar Rasha
A nata bangaren rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun samu nasarar kashe sojojin Rasha kusan 50 tare da lalata jiragen yakinsu 6 yayin gumurzun da bangarorin biyu ke yi, tun bayan da Rashan ta kaddamar da yaki kan makwafciyar tata a wannan Alhamis.
Tuni dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ayyana dokar ta-baci a ilahirin fadin kasar, tare da yin kira ga jama’a da su bada gudunmawarsu ga yakin da ya barke tsakaninsu da Ukraine.
Gwamnatin Ukraine ta ce fararen hula da dama sun rasa rayukansu sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan kasar, inda ta kara da cewar za a ba da makamai ga duk wanda yake so.
Yaki ya barke tsakanin makwaftan biyu ne bayan da ‘yan aware da ke samun goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine suka bukaci taimakon gwamnatin Moscow.
Tuni dai kasashen yammacin Turai suka yi tir da matakin Rasha na kaddamar da yaki akan Ukraine.
Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya kira Putin a matsayin mai mulkin kama karya kuma ya yi gargadin cewa yanzu kasar za ta fuskanci gagarumin takunkumi daga yammacin Turai.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun lalata kayayyakin yaki na sama a kasar Ukraine, ciki har da jiragen sama 11, inda rundunar ‘yan sandan Ukraine ta ce ana kai hare-hare a duk fadin kasar.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta goyi bayan Ukraine sannan ya yi gargadin cewa mamayewar da Rasha ta yi wa makwabciyarta zai haifar da da na sani ainun.
Rahotanni dai na cewa Sojojin Rasha na kokarin kutsawa cikin yankin Kyiv da kuma yankin Zhytomyr da ke kan iyakar Belarus, in ji jami’an kan iyakar Ukraine.
Babban Kwamishinan ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa halin da ake ciki a Ukraine na kara tabarbarewa cikin sauri tare da yin kira ga kasashe makwabta da su bude iyakokinsu ga mutanen da ke neman mafaka.
Kungiyar tsaro ta NATO ta ce ba ta da sojoji a cikin Ukraine kuma ba ta da shirin aikewa da kowa cikin kasar.