Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kira ga takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, da ya mika wuya dangane da yakin Ukraine domin kada yakin ya fadada ya karade duniya.
Macron ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, inda ya ce “Ba mu bukatar Yakin Duniya.”
- Kotu ta tsare wanda ya kashe matashi a gidan yari
- Wayar baturen da ta bace a Ingila ya gano tana Najeriya bayan wata guda
Ya ce “Muna kokarin taimaka wa Ukraine ta kare kanta, kada ta kai wa Rasha hari.
“Wajibi ne Vladimir ya dakatar da wannan yakin haka, sannan ya martaba iyakokin Ukraine,” in ji shi.
Kazalika, Macron bayyana ci gaba da taimaka wa Ukraine da makamai da Faransa ke yi don karfafa mata wajen kare kanta daga hare-haren Rasha.