Rikicin da sojojin Rasha suka yi a yaƙi da Ukraine ya kai ga rasa mutum 50,000, a cewar wani bincike.
Rahoton sashen Rasha na BBC wanda ya yi nazari da ƙirga mace-mace tun bayan da sojojin Rasha suka mamaye Ukraine da ke maƙwabtaka da ita a watan Fabrairun 2022, ya bayyana adadin a ranar Laraba, tare da cewa adadin mamatan ya ƙaru a shekara ta biyu na rikicin.
Ƙididdigar ta BBC a Rasha ya ambato kungiyar yaɗa labarai mai zaman kanta ta Mediazona da masu aikin sa kai suna cewa yawan waɗanda suka mutu ya haura dubu 27 da 300 a shekara ta biyu na yaƙin, wanda ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 a shekara ta farko.
Rahoton waɗanda suka mutu a hukumance ɗaya tilo da Rasha ta fitar ya ce a watan Satumban 2022 an kashe sojojinta ƙasa da 6,000.
Binciken ya ce fursunoni 9,000 da aka ɗauka a matsayin sojojin haya na Wagner ko kuma kai tsaye ta Ma’aikatar Tsaro, an kashe su a rikicin.
BBC ta kara da cewa bayananta ba su bayar da labarin asarar rayuka da aka samu a tsakanin dakarun sa-kai a Donetsk da Luhansk a gabashin Ukraine ba, sannan yawan waɗanda suka mutu a zahiri ya zarce 50,000.
Ukraine ta ce a watan Fabrairu ta yi asarar sojoji 31,000.