✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin mallakar fili na yin barazana ga bunkasar hakar ma’adinai

Rikicin mallakar filayen hakar ma’adinai a sakanin jihohi da gwamnatin tarayya na daga cikin abin da ke ci wa masu ruwa da tsaki a harkar…

Rikicin mallakar filayen hakar ma’adinai a sakanin jihohi da gwamnatin tarayya na daga cikin abin da ke ci wa masu ruwa da tsaki a harkar hakar ma’adinai tuwo- a- kwarya.
Matsalar na kawo cikas ga bunkasar hakar ma’adinai cikin gaggawa a lokacin da gwamnatin Shugaba Buhari ke kokarin bunkasa bangaren don rage dogaro da man fetur a kasar.
Da dama daga masu lasisin hakar ma’adinai na fuskantar kalubale wajen hakar ma’adinan sakamakon matsalolin da suke fuskanta daga mazauna yankunan da suke zaune a filayensu.