Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta yi babban taron lalubo mafita ga rikicin siyasar da ya barke a kasar Mali.
Shugaban Majalisar Shugannin Kasashen ECOWAS, Mahamadou Issoufou na Nijar, ya ce babban taron zai gudana a ranar Litinin 27 ga Yulin ta bidiyo.
Ya bayyana haka ne bayan taron tattaunawa da aka yi a Bamako, babban birnin kasar Mali a ranar Alhamis.
Taron ya samu halarcin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da mai masaukin baki, wato Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.
Sauran su ne Machy Sall na kasar Senegal, Nana Akufo-Addo na Ghana da kuma shugaba Alassane Ouattara na kasar Cote d’Ivoire.
Gabanin taron Shuganninn kasashen sun saurari jawabi daga manzonta na musamman kan rikicin, tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da shugaban ‘yan adawan kasar Mali, Imam Mahmoud Dicko.
Taron ya kuma saurari bayanai daga wakilan gamayyar jam’iyyun adawa ta M5 da kungiyoyin fararen hula.
Shi ma Shugaba Keita, ya yi wa taron jawabi kan matsalar da ta haifar da rikicin siyasar, musamman abin da ya haddasa zanga-zangar da daga bisani ta kazance.
Bayan taron na ranar Alhamis, shugaban na ECOWAS ya ce kungiyar za ta yi dukkan mai yiwuwa domin kawar da rikicin na Mali.
Ya ce sun yi ittifakin cewa dole bangarorin da ke rikicin su sadaukar da kai domin wanzar da aminci a kasar.
Sun nuna damuwa cewa rashin magance matsalar za iya sa rikicin yaduwa zuwa kasashe makwabtan Mali.
A nasa bangaren, Shugaban Kasar Ghana, a cikin wata sanarwa ya ce kungiyar za ta tabbatar an bi ka’idojinta wajen kafa gwamnati domin samun zaman lafiya a yankin.