✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci ya barke a Taraba

A watan Mayu na wannan shekarar ce mummunan fada ya barke a tsakanin kabilun biyu.

Sabon rikicin kabilanci ya barke tsakanin kabilun Karimjo da Wurkum a Karamar Hukumar Karim-Lamido da ke Jihar Taraba.

Ana zargin ’yan kabilar Karimjo da kai hari a kauyukan Wurkum a daren jiya Asabar.

Wata mijiya ta shaida wa Aminiya cewa mayakan sa-kai ’yan kabilar Karimjo ne suka kai hare-hare a kauyukan Wurkunawa.

A lokacin hare-haren da aka kai an kona kauyuka sama da biyar tare kone kayan abinci da ababen hawa da sauran wasu kayayyakin na miliyoyin Naira.

A watan Mayu na wannan shekarar ce mummunan fada ya barke a tsakanin ’yan kabilar Karimjo da Wurkum a sakamakon nada Sarkin Wurkum wanda tsohon gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ya yi.

’Yan kabilar Karimjo na kalubalantar nada Sarkin wanda fadarsa ke cikin Karim-Lamido wanda ’yan kabilar Karimjo ke cewa garinsu ne.

Bayanai na cewa an yi asarar rayuka masu yawan gaske tare da kone dukiya mai yawan gaske a rigimar wancan lokaci.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi zaman sulhu tsakanin Dattawan Wurkunawa da Karimjawa da nufin yi wa tufkar hanci amma kuma sai aka sake samun barkewar fada tsakanin kabilun biyu.

Kakakin rundunar ’yan sanda Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar  lamarin, sai dai bai bayyana adadin asarar rayukan da aka yi ba.