✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Hausawa da Yarbawa ya barke a Legas

Ana zaman dar-dar bayan sake barkewar rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Yarbawa a unguwar Fagba, Iju Ishaga ta Jihar Legas. Tashin rikicin a ranar Juma’a…

Ana zaman dar-dar bayan sake barkewar rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Yarbawa a unguwar Fagba, Iju Ishaga ta Jihar Legas.

Tashin rikicin a ranar Juma’a ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama tare da kona gine-gine, ko da yake ba a kai ga gano ko an samu asarar rai ba.

Aminiya ta gano cewa tun tashin hankali ya samo asali ne bayan ‘yan daba da ke zanga-zangar #EndSARS sun kai wa direbobin motocin shanu da yaransu hari inda suka kashe mutum tara ranar Talata.

Wani mazaunin unguwar ya ce, “Tun ranar Talata aka fara fadar; Mun dauka komai ya wuce, amma kawai sai muka ga abin ya sake dawowa yau”.

Abin da ya faru

Wani shaida, Muhammad Tom, ya ce tsagerun sun far wa direbobin ne a lokacin da aka ba su hanya, suna kokarin shigar da su kasuwar ta Abbatuwa.

Bayan haka ne a ranar Laraba Sarkin Fulanin Kasuwar Abbatuwa da ke Oko-Oba a Legas, Alhaji Muhammadu Danmubaffa ya roki ‘yan Arewa a kasuwar da su kai zuciya nesa.

Barnar da aka yi

Ya shaida wa Aminiya cewa, zuwa safiyar Laraba, 21 ga Oktoba, sun tattaro gawarwakin direbobin manyan motocin shanu da yaransu akalla guda takwas, wasu an kone su kurmus, baya ga wadanda aka raunata.

“Mun karbo takarda daga wajen ‘yan sanda domin mu yi musu sutura a makabartar garin Agege.

“Akwai wadanda aka gane ‘yan uwansu akwai kuma wadanda an kone su kurmus.

“Baya ga wadanda aka rasa an kone manyan motocin shanu biyu da kuma motar tanka guda an kuma farfasa guda bakwai.

Manya sun sa baki

“Sarkin Fulanin tare da ragowar shugabannin Jama’a sun yi taro da al’ummarsu domin kwantar masu da hankula tare da kiyaye faruwar tarzoma.

“An kuma nada wakilai domin ganawa da shugabanin Yarbawan yankin domin tabbatar da an zauna lafiya”, inji shi, a ranar Laraba.

Sai dai duk da haka jama’a sun ci gaba da zama cikin zullumi tun bayan da zanga-zangar lumana ta #EndSARS ta juye ta koma tashin hankali inda tsageru kone kadarorin gwamnati da dukiyoyin daidaikun jama’a.