Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya soki shugabannin jam’iyyar APC kan rashin yi wa Buhari da Fulani adalci game da rikicin Fulani.
Lamido ya koka kan yadda ake wa Fulani wani kallo na daban duk da cewa mutane ne masu son zaman lafiya.
- Saraki ya gargadi Buhari kan rikicin Fulani da Yarbawa
- Muna kan binciken wadanda suka kona gidan Sarkin Fulanin Oyo – ’Yan sanda
- Yadda aka kai wa Fulani hari a Oyo
“Ka je kafofin sada zumunta ka ga yadda suke fadar maganganu na rashin adalaci kan Fulani, saboda namu ne yake shugabancin Najeriya; Amma lokacin da Jonathan yake Shugaban Kasa ai ba haka suke yi ba.
“Shirun Tinubu, Amaechi, Rochas, da Chris Ngige kan rikicin Fulani ya nuna kiyayyarsu ga Fulani a zahiri.
“Tinubu ya san ban zabi Buhari ba, amma tunda ’yan Najeriya sun zabi Buhari, me ya hana su fitowa su kare Buharin a lokacin da ya kamata?
“Me yasa ’yan jam’iyyar APC da suka zabi Buhari a 2019 ba su kare shi a yanzu ba, sai suka yi shiru saboda munafunci?”
A yayin jawabin nasa ga manema labarai a Kano a ranar Laraba, Sule Lamido ya ce tsanar da aka yi wa Fulani a Ondo da Oyo ya samu asali ne daga irin gazawar gwamnati mai ci ta Shugaba Buhari.
A cewarsa, yanzu an yi wa Fulani wata mummunar lamba a matsayin muggan miyagun al’umma.
Ya kuma ce matsalar garkuwa da mutaneda ta’addanci a fadin Najeriya ya samo asali ne daga rashin samun shugabanci nagari.
Sannan ya ce Arewancin Najeriya na bukatar agaji duba da yadda matsalar tsaro ta addabi yankin.