✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Boko Haram ya yi ajalin mutum 35,000 a Arewa maso Gabas – MDD

Hukumar ta ce kashe-kashe sun fi muni ne a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce kimanin mutum 35,000 ne suka mutu tun fara rikicin Boko Haram daga shekara ta 2009 zuwa watan Agustan 2023.

Shugaban ofishin hukumar a Jihar Adamawa, Elsie Mills-Tetty ce ta bayyana hakan yayin wani taron horar da sojoji a kan kare hakkin bil Adama da kuma kare fararen hula a Yola ranar Laraba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa hukumar ta shirya taron ne domin ba su horo kan hanyoyin kiyaye hakkokin jama’a yayin ayyukansu.

Elsie, wacce wani Jami’i a hukumar, Umar Abdullahi ya wakilta, ta ce sun tattara alkaluman ne daga rahoton wata cibiyar kasa da kasa mai suna GCRP na watan Agustan 2023.

Ta ce illar da rikicin ya yi wa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar mazauna Jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ma Najeriya baki daya, ba za ta misaltu ba.

Jami’ar ta ce a shekara ta 2022, wani binciken hukumar ya bayar da rahoton take hakkin bil Adama da kuma hanyoyin magance su.