✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Biyafara: An yi taron zaman lafiya a LegasAbbas dalibi, a Legas

Shuwagabanin al’umma a Jihar Legas sun shirya taron zaman lafiya a tsakanin ƙabilun yankin, waɗanda suka haɗa da Yarabawa da Hausawa da Ibo, domin hana…

Shuwagabanin al’umma a Jihar Legas sun shirya taron zaman lafiya a tsakanin ƙabilun yankin, waɗanda suka haɗa da Yarabawa da Hausawa da Ibo, domin hana afkuwar irin rikicin da ya faru a makon jiya a Jihar Abiya, wanda aka danganta da ƙungiyiar nan mai tada ƙayar baya ta masu karajin kafa ƙasar Biyafara, rikicin da ya rutsa da wasu ’yan Arewa mazauna Kudu Maso Gabas da ma Yarabawa mazauna yankin, inda rahotanni suka tabbatar da salwantar rayukansu da kone masu wuraren ibada.

Babban basaraken Yarabawa na Lardin Ojora da Igammu, Oba Abdulfatah Aromire ne ya shirya wannan taro a fadarsa a karshen makon jiya, taron da ya sami halartar al’ummar Hausawa da Yarabawa da na Ibo tare da shuwagabanninsu da jami’an tsaro; inda masana ta fuskar tsaro da shuwagabannin gargajiya suka gabatar da jawaban bayyana mahimmancin zaman lafiya tare da guje wa tayar da tarzoma. Basaraken ya shaida wa Aminiya cewa, a duk lokacin da irin wannan lamari ya taso na halin ɗar-ɗar a wasu sassan ƙasar nan, yakan kira taron zaman lafiya makamancin haka. Ya ce a yanzu lokaci ne da ya kamata ’yan Najeriya su so juna, su yi aiki tare domin gina ƙasa ba tare da nuna bambance-bambace ba.

A zantawarsa da Aminiya, Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun, wanda tsohon jami’in tsaro ne, ya bayyana muhinmmancin taron. Ya ce wannan shi ne karon na biyu da suka gudanar da irin taron a ’yan kwanankin nan. “Domin a baya ma da aka taɓa kama dan Boko Haram a wannan unguwa, hankalin jama’ar yankin ya tashi ƙwarai har sai da babban basaraken wannan yanki ya kira kwatankwacin wannan taro, inda aka faɗakar da jama’a aka kuma kwantar masu da hankali. Ka san ƙarmar hukumarmu ce ta fi kowacce tarin ƙaɓilu daban-daban, da ƙabilun ƙasashen Ghana da Nijar da Togo da sauran ƙasashen Afirka,” inji shi.

Alhaji Adamu Nabi ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ƙwararan matakan da ya ɗauka a jihohin Kudu Maso Gabas. Ya ce lamarin tsaro ba abu ne da ake yi wa riƙon sakainar kashi ba. Ya shawarci ’yan Najeriya da su zamo masu son zaman lafiya tare da bin doka a duk inda suke. Ya ce abin a yaba ne yadda sauran al’ummar yankunan ƙasar nan, musamman Arewa suka kauda kansu daga barin ɗaukar fansa a kan abin da aka yi wa ’yan Arewa a wasu jihohin Kudu Maso Gabas. Ya ce hakan ya yi daidai domin jama’a sun bai wa gwamnatin ragamar ɗaukar matakan da suka dace kuma cikin ikon Allah gwamnatin ta shawo kan lamarin.