Jam’iyyar APC na cikin rikicin shugabancin da ba kasafai jam’iyyar siyasa kan shiga irinsa ba ta fita ba tare da tabo ko tarwatsewa ba. Shin ko Shugaban kwamitin riko, Gwamna Mai Mala Buni zai iya ceto jam’iyyar?
Wasu na ganin kusan irin abun da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga ke nan a shekarun baya da ya kaita ga faduwa zaben 2015, bayan bangarewar da wasu jiga-jiganta suka yi da suka hada da gwamnoni biyar.
Irin wancan rikicin mai kamanceceniya da wanda ya wargaza jam’iyyar PDP ya dade da fara kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki.
Mafi kusa shi ne, rikicin tantance halastacen shugaban rikon kwarya, wanda ya faru sakamakon dakatarwar da Kotu ta yi wa Shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole.
- Buhari ya karbi gurguwar shawara kan taron NEC —APC
- Yadda Oshiomhole ya mika wuya ga NEC din Giadom
- Sabuwar baraka a APC kan janye dakatar da Oshiomhole
Wannan rikici dai ya faro ne daga jihar Edo, watau cibiyar shi Oshiomhole sakamakon rashin jituwarsa da Gwamna Godwwin Obaseki wanda daga karshe aka yi ba wan ba wan.
Oshiomhole dai aka dakatar da shi daga jam’iyyar, shi kuma Obaseki aka hana Obaseki shiga takarar zaben fitar da gwani a karkashi jam’iyyar, wanda hakan ya kai shi ga sauya sheka domin samun damar yin takara a karkashin PDPn.
Babban nakasu da rikicin ya haifar wa jam’iyyar shi ne tunzura rarrabuwar kai da dama can akwai shi cikin jam’iyyar, har ta kai ga an kasa tantance wa ke da alhakin rikon jam’iyyar.
Wasu na ganin cewar Shugaba Buhari da ka iya kashe wutar da ruwa cikin kofi bai yi hakan ba sai da ta yi ruruwar da ko an kashe ta, ta riga ta yi lahani ga wasu sassan jam’iyyar.
Kyakkyawar alakar Buni da bangarori
Wannan ya sa ake ganin kawo Gwamna Mai Mala Buni, wanda tsohon Babban Sakataren Uwar Jam’iyyar ne zai yi tasiri sakamakon sanin jam’iyyar da ya yi da mukarrabanta da kuma zaman lafiya da ya yi da su lokacin da yana cikinsu.
Haka nan wasu na ganin ya shiga cikin sasanci da zabubbuka iri daban-daban da ya kai jam’iyyar ga nasara, kai har ma da zaben 2019, da a lokacin wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da shugabannin Majalissar Tarayya Bukola Saraki da Yakubu Dogara da manyan sanatoci suka bangare zuwa jam’iyyar PDP bisa korafin ba a yi musu adalci.
Gwamna Buni, a bayaninsa na karbar ragamar rikon kwaryar Jam’iyyar, ya ce zai yi adalci ga duk wani dan jam’iyyar domin ganin an daidaita bisa ainahin harsashin da aka gina ta a kai, tare da kokarin gudanar da sahihin zaben shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar.
Tsugune ba ta kare ba
Kafin a je ko’ina, Shugabannin rikon da aka rushe gwamna Buni ya hau na ganin cewa babu adalci a matakin da aka dauka kuma suka yi kunnen uwar shegu da kiran da Shugaba Buhari ya yi na cewar duk wanda ya kai kara kotu ya janye.
Shi wannan bangare da Hilliard Eta yake jagoranta ya yi koken cewar taron wanda abokin hamayyarsu Giadom ya shirya aka kuma rushe kwamitin rikonsu ba halastacce ba ne duk da ya samu halarcin shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin Majalisar Tarayya.
Suka kuma yi dogaro da cewar Shugaban jam’iyya ne kadai zai iya kiran taron kuma sai ya ba da wa’adin kwanaki goma sha hudu (14), domin haka suka tuntubi lauyansu domin su san matakin da za su dauka.
Wasu na ganin wannan matakin da za su dauka ka iya kara dagula kudirin kawo karshen matsalolin jam’iyyar da Gwamna Mai Mala yake kokarin kawowa.
Shirin ko-ta-kwana
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana wa Aminiya cewar shugaban kasa da gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar na nan sun kakkabe “Article 21 (V)” na kundin tsarin jam’iyyar da zai ba da damar dakatar da korarren Kwamitin Zartarwar idan har suka kai kara kotun.
Hakan ya sa wasu daga cikin kwamitin da aka rushe suka yi mubaya’a ga kwamitin riko na Mai Mala Buni.
Mafitar na tsakanin Buhari da Tinubu
Sai dai kuma a ra’ayin wasu, matsalar jam’iyyar ba aba ce da kwamitin zai iya magancewa ba, musamman idan aka yi la’akari da jita-jitar da ake yi ta cewar kwamitin zartarwar da aka rushe magoya bayan Oshiomhole ne, wanda kuma bisa zargi, abin da ya yi Oshiomhole shi ya yi Uban Jam’iyyar APC, watau tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.
Tunanin hakan ya sa mutane suka fi karkata cewa sasancin jam’iyyar na nan tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne silar hadakar Jam’iyyar ta APC da kuma lashe zaben da Buhari ya yi a shekarar 2015.
Wasu kuma na ganin cewar duk badakalar da ake yi rikicin share fage ne na wa zai daga tutar jam’iyyar APC don zama dan takarar shugabancin kasa a shekarar 2023. Tuni dai ake rade-radin cewa Tinubu zai fito takarar sai dai bai fito karara ya bayyana niyyarsa ba.
Sai dai kuma wasu na ganin cewar ko da babu matsala tsakanin Tinubu da Buhari, fitowa fili da Buhari ya yi ya goyi bayan kwamitin riko na Giadom da kuma sanya baki wajen rushe kwamitin riko na Hilliard Eta da ake zargi ‘yan barandan Oshiomole ne wani sabon salo ne a cikin jam’iyyar.
Kalubalen da Buni zai fara fuskanta
Bayan karbar jan ragamar Jam’iyyar da ya yi, akwai ababan da ake sa ran Nuni zai aiwatar cikin gaggawa da suka hada da: Sasanci tsakanin bangarorin adawa a cikin jam’iyyar da hada kan ‘yan jam’iyya da fuskantar nasarar zaben Edo da gudanar da sahihin zaben shugabanin jam’iyyar sai kuma kokarin mayar wa jam’iyyar martabarta.
Sanin kowa ne cewar a karkashin shugabancin Oshiomhole, jam’iyyar ta APC ta rasa Jihar zamfara da Bayelsa da wasu zababbun mukamai salin alin saboda sakaci da rashin samun shugabanci da ya dace.
Shugaban kasa da Gwamnoni za su zabi shugaban jam’iyyar
Ana sa ran Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnonin APC za su zabi sabon shugaban jam’iyyar.
Wata majiya ta tabbatar wa wakilinmu cewar gwamnonin da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun aminta da a yi maslaha wajen zaben wanda zai shugabanci jam’iyyar ne domin kauce wa damka jam’iyyar hannun wani ko wasu tsirarun mutane.