✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin APC Kano: Na San Wanda Ya Sa ’Yan Daba Su Kawo Min Hari —Doguwa

Doguwa ya ce ya yi mamakin harin musamman saboda Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya riga ya yi musu sulhu da Murtala Sule Garo

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alhassan Doguwa, ya ce ya san wadanda suka daukin nauyin ’yan ta-kifen siyasa da suka kai wa tawagarsa hari a filin jirgin Malam Aminu Kano.

Ya ce baya ga harin filin jirgin, sai da ’yan barandan siyasara suka ragargaza motarsa, suka raunata magoya bayansa da dama, sannan suka sace motarsa a unguwar Gandun Albasa, kusa da gidan Bashir Tofa.

Doguwa ya ce ya yi mamakin harin musamman saboda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya riga ya yi musu sulhu da dan takarar mataimakin gwamna na APC, Murtala Sule Garo, wanda a baya suka yi takun saka da shi har ya kwada masa kofin shayi.

“An lalata min fastocin kamfen da  a daidai kofar shiga filin jirgin sama na Kano, kuma an lalata min mota; To na san wadanda suka turo ’yan ta-kife aka yi min barna, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, ”An sassari da dama daga magoya bayana; wasu guda uku har yanzu na asibiti kwance, wasu ukun kuma an sallame su, aannan an sace min mota.”

Sai dai ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, kada su dauki doka a hannunsu ko ramuwar gayya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Shugaan Jam’iyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya sanar a ranar Talata an yi sulhu tsakanin Doguwan da Garo kuma sun yafe wa juna.

Mun tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, inda ya ce ba shi da masaniyar ko an kai lamarin ga ofishin ’yan Sanda ko a’a.