A ranar Litinin mai zuwa ne uwar jam’iyyar APC ta kasa za ta raba mukamai ta hanyar yin maslaha a reshenta na Jihar Kano tsakanin tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje da na Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau.
Kakakin Sanata Shekarau, Dokta Sule Ya’u Sule, ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawarsa da Aminiya ta wayar salula ranar Lahadi.
Ya ce hakan na cikin matsayar da aka cimma a tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu ranar Lahadi.
Kwamitin riko na APC na kasa karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci taron sulhun, yayin da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara suka halarta.
Tattaunawar bisa alamu ita ce za ta kawo karshen sa-toka-sa-katsin da aka shafe tsawon lokaci ana yi a tsakanin bangarorin biyu, da zarar an fitar da rabe-raben ranar Litinin.
Doka Sule ya ce, “Da mu da su kowa ya fadi matsayinsa, shi ne aka samu daidaito cewa za a yi maslaha, wacce kuma za ta dadada wa kowa.
“An kafa wani kakkarfan kwamiti, kuma zai zo Kano don ya tabbatar an yi abin da ya dace ranar Litinin,” inji shi.
Aminiya ta rawaito cewa tuni dai rikicin jam’iyyar ya kai bangarorin biyu zuwa gaban kotu, yayin da tsagin Sanata Shekarau ya yi nasara a babbar kotu.
Sai dai sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin, tuni tsagin Gwamna Ganduje ya daukaka kara, wacce ta dage ranar yanke hukunci.
Abin jira a gani shi ne ko wannan yunkurin na uwar jam’iyyar zai iya kawo karshen dauki-ba-dadin da aka jima ana yi.