Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya fasa yin takarar Sanatan Kano ta Arewa bayan ya sasanta da wanda yake kan kujerar, Sanata Barau Jibrin a rikicin jam’iyyar APC na Jihar.
Barau dai na daya daga cikin jagororin kungiyar tafiyar G-7, karkashin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, wacce ta fatata rikicin Shugabanci da tsagin Gwamna Ganduje.
- Wata ta sake yin batanci ga Annabi a Maiduguri
- Amarya da ango da wasu mutum 40 sun kwanta bayan cin abincin biki a Afghanistan
Tuni dai Barau ya sayi fom din dake tsayawa takarar kujerar ta shi, a daidai lokacin da ake rade-radin Ganduje shi ma ya saya.
Sai dai majiyoyi sun shaida mana cewa yanzu Ganduje ya fasa tsayawa takarar, inda ya amince Barau ya ci gaba da neman kujerar, bayan an yi sulhu a tsakani.
Da yake tabbatar da labarin, Sakataren APC a Jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya ce tattauanawar ta yi nasara.
Tun bayan rashin nasarar da tsagin na G-7 ya yi a Kotun Koli, mambobin kungiyar da dama sun sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP, yayin da rahotanni ke cewa hatta Sanata Shekarau ya kammala shirin komawa can.
Sai dai a makon da ya gabata Sanata Barau Jibrin ya ce yana nan a cikin jam’iyyar ta APC kuma yana nan a kan bakar shi ta sake neman takarar.