Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kofar yin sulhu a bude take tsakaninsu da tsagin Sanata Ibrahim Shekarau.
Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC, inda ya ce yanzu lokaci ne na tafiya tare da mayar da hankali kan harkokin ci gaban jam’iyya.
A makon da ya gabata ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da Abdullahi Abbas na tsagin Ganduje a matsayin sahihin Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano, bayan kwashe tsawon lokaci ana fama da rikicin shugabannci tsakanin tsaginsu da na Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau.
A cewar Ganduje, “Muna rokon ’yan uwanmu su zo a hada kai baki daya don a yi wannan tafiya tare, sannan kuma ina so na sanar da ’yan jam’iyya cewa a daura damara don yanzu za a shiga gwagwarmayar zabe.
“Yana da matukar muhimmanci shugabannin jam’iyya su san aikinsu ta yadda za a tafiyar da jam’iyya a kan tafarkin dimokradiyya,” cewar Ganduje.