Ko shakka babu Najeriya cike take da abin mamaki idan har kana bibiyar al’amuran yau da kullum, Najeriya ce kasa daya tilo wadda a ka fi samun rikice-rikice tsakanin al’umma mabambanta, duk lokacin da wata hatsaniya zata barke in za ka bincika za ka ga tsakanin al’umma mabambantan addinai da kabilu take tashi, duba da irin yadda malamai suke tashi tsaye tsayin daka wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a cikin kasa, amma duk da hakan abin yakan ci-tura, inda ake yawan samun rashin jituwa a duk lokacin da wani abu ya tashi, akan samu mummunar tashe-tashen hankula. Hakan ya kan yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da samun jikata, a tsakanin wadanda rikicin ya tashi a tsakaninsu, kai wani lokacin abin ma yakan shafi wanda ba su ji ba su gani ba.
Rikicin kabilanci wani babban kalubale ne wanda ya zama ruwan dare a nan Najeriya wanda ya kamata tun daga masu unguwanni hadi da sarakunan gargajiya ta kowane bangare da an majalisun jihohi da shugabannin kananan hukumomi da ’an majalisun tarayya hadi da sanatocinmu na kowane bangare da gwamnonin kowane yanki hadi da jami’an tsaro, su hadu waje daya domin ganin an magance wannan matsalar gaba daya a cikin wannan kasa,
Saboda batun na zaman lafiya ne, to ya shafi kowa da kowa, domin ana son samun gudunmuwa ta kowane ɓangare dan a gudu tare a tsira tare, kamar yadda ake fada Najeriya kasa daya uwa daya uba daya al’umma daya inji wani mawaki, amma dai gaskiya mu ba mu ga alamar hakan ba.
Domin kuwa babu wata kasa wanda zata ci gaba a duniya face an samu hadin kan ’an kasa wajan samun yilwatacen zaman lafiya ta kowane fanni, kasancewar zaman lafiya shi ne babban abin da duk wani dan ƙasa yake so, saboda sai ansamu zaman lafiya sannan arziki zai sallamo a cikin ƙasa, kowa ya wadata har wata kasa ta yi sha’awar shigowa a ciki domin taruwa waje daya a habaka arzikin kasa,
Duba da ganin irin yadda wadanda suka riki Najeriya tun farko yadda suka ba da gudunmuwa dari bisa dari suka tsayu suka ba da rayuwarsu da lokacin su, domin kawai ganin kasar nan ta kai a duk inda ake so. Kuma sun yi hakan ne ba don tara abin duniya ba aa sai dai kawai domin ganin ta zama kasa daya mai cin gashin kanta, har suka bar duniyar nan ba su tara wani abin a zo a gani ba. ta gefen tara abin duniyar da za su amfana da shi ko ‘ya’yansu. Shin me ya sa mu ba za mu ba da tamu gudunmuwa ba domin ganin ta ci gaba da kasancewa kasa daya mai cikakken Ikon fada aji a duk fadin Afirka? Kasancewar Najeriyar ita ce uwa ga Afrika.
Rikici tsakanin Fulani da makiyaya rikici tsakanin addinai da kabilanci. Mu ke nan a hjaka? Shin ba za mu hada kanmu ba, domin samun dimbin arzikin da Allah ya wadata mu da su? Babban abin la’akari a nan shi ne yadda wasu manyan shugabanni suka zuba ido a na ta tafka ta’asa, babu tsawata wa.
Da wannan muke kira da babbar murya ga shugabannin kasa da wadanda alhakin tsawatarwa ya rataya a wuyansu da su yi duk mai yiyuwa domin ganin komai ya daidaita, an ci gaba da samun zaman lafiya mai ma’ana ta kowane fanni.
Da wannan muke kira ga an Najeriya kwata! da muhadu domin gina wannan kasa tamu mai albarka. Domin mu gudu tare mu tsira tare. Allah Ka taimaki Najeriya da zaman lafiya da arziki madauwami, da yankin Afrika gaba daya.
Mai Apple Gusau dan Qungiyar Muryar Talaka ta kasa reshen Jihar Zamfara. 08133376020/08086679022