Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na kudancin Najeriya kuma Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, ya dakatar da Sarkin Zabarmawan Ikeja Alhaji Husaini Sarki tare da soke nadin Sarakunan Zabarmawa bakwai da aka yi cikin makon jiya a Legas.
Sai dai Sarkin Zabarmawan na Ikeja Alhaji Husaini Sarki ya ce ba za ta sabu ba domin Fadar Sarkin Sasa ba ta da hurumin shiga cikin al’amuran da suka shafi kabilun Zabarmawa.
- An min tayin miliyan 150 da mota don na koma tafiyar Tinubu amma na ki — Sarkin Waka
- Mun yi wa dalibai miliyan 1.1 rajistar jarabawar UTME a bana – JAMB
Bayanin dakatar da Sarkin Zabarmawan na Ikeja da soke nadin Sarakunansu dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga Fadar Sarkin Sasa a ranar Asabar.
A cewar sanarwar, mai dauke da sa hannun Sarkin na Sasa, wacce aka aika wa Sarkin Zabarmawan na Ikeja, “Daga yau [Asabar], 11 ga watan Fabrairun 2023, Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na kudancin Najeriya ta dakatar da kai daga kiran kanka a matsayin Sarkin Zabarmawan Ikeja kuma Wakilin Sarkin Zabarmawan Najeriya.
“Duka nade-naden da Sarakunan Zabarmawa bakwai da ka yi a Legas daga yanzu an soke su. Kaje ka mika kanka ga Fadar Sarkin Yakin Jihohin Yamma, Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan domin binciken zargin da ake yi maka,” in ji sanarwar, wacce ba ta yi cikakken bayanin dalilin daukar matakin ba.
Da Aminiya ta tuntubi Sarkin Zabarmawan Ikeja Alhaji Husaini Sarki a kan lamarin, ya ce sam fadar Sarki ba ma ta da hurumin shiga harkokinsu, ballanata ta kai ga warware nadin da ta yi.
Ya ce, “Da farko dai al’ummar Zabarmawa mazauna Jihar Legas muna girmama Sarkin Sasa a matsayinsa na ubanmu, amma ina tabbatar maka cewa Fadar Sarkin Sasa ba ta da hurumin shiga cikin lamarin da ya shafi al’ummar Zabarmawa zalla domin bai shafe ta ba.
“Wannan al’amari ne da ya shafi kabilar Zabarmawa kadai da muke nada Shugabanninmu da kanmu. Ka ga babu yadda Zabarmawa za su shiga cikin nadin Shugabannin wasu kabilu kamar Hausawa ko Fulani ko Yarbawa ko Nufawa da Ibira da makamantansu.
“Tun da haka ne me zai sa wata kabila ta shigo cikin lamarin kabilar Zabarmawa? Har zuwa lokacin da nake amsa tambayarka wannan takarda da aka ce an aiko min ba ta iso gare ni ba.
“Kuma idan takardar ta iso wurina ba ni kadai zan yi aiki a kanta ba domin akwai Majalisar ci gaban Zabarmawan Legas da ita ce take da alhakin daukar matakin da ya dace a kan wannan lamari.
Tun da farko sai da Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya karrama Sarkin Yakin Jihohin Yamma, Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan da Sarkin Zabarmawan Jihohin Yamma Alhaji Aliyu Abubakar da lambar yabo mafi girma a masarautar Sasa saboda irin rawar da suke takawa ta fannin hada kan ’yan Arewa mazauna kudancin kasa da ci gabansu.
Sarkin na Sasa ya yi amfani da wannan dama wajen nada wa jikokinsa bakwai masu shekaru daga takwas zuwa 15 rawani da mika masu takardar tabbatar da nadinsu a matsayin masu rike da sarautun gargajiya.
Malaman addinin musulunci da suka halarci wajen bikin sun yi wa kasa addu’o’in samun zaman lafiya da fatan yin zabe mai zuwa lafiya.