Olubadan, Oba Olalekan Balogun, ya dakatar da Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin kan zargin rashin biyayya.
Olu na Ibadan ya dakatar da Sarkin Sasa ne ta hannun Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Zungeru, bisa zargin bayar da sarautu ba tare da tuntubar Sarkin Hausawan ba.
- An tsare hedimasta kan fyade ga ’yar shekara 4 a makaranta
- Yadda Cin Abinci Sau 3 Ke Gagarar Masu Aikin Albashi
An sanar da dakatarwar da aka yi wa Sarkin Sasa, wanda Hakimi ne a Masarautar Al’ummar Hausawa a Jihar Oyo ne a wani zama da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Zungeru ya jagoranta a Sabo Ibadan.
Sarkin Hausawan ya yi zargin cewa zaman Hakimin na iya haifar da rikici a yankin, don haka aka dakatar da shi har zuwa lokacin da Majalisar Al’ummar Arewa da ke Ibadan ta yanke hukunci kan lamarinsa.
“A zamanin wana, Shuaibu Dikko III, a 1983 aka nada Alhaji Haruna Maiyasin a hakimi, wato Baale a kasar Yarbawa domin samun zaman lafiya da adalci a tsakanin al’ummar Hausawa da ke Sasa.
“Saboda haka, kuma don guje wa kowane irin rikicin kabilanci irin na Sabo-Sagamu, Sabo-Ile-Ife da kuma na Sasa da ke Karamar Hukumar Akinyele, ni Alhaji Ali Zungeru, Sarkin Hausawa Ibadan da Majalisar Masarautar Arewa muka dakatar da Maiyasin daga hakimcin Hausawan Sasa,.
“Dalili shi ne saboda rashin ladabinsa, raina kujerar Sarkin Ibadan, da kuma ba da sarautun da yake yi ba tare da sahalewar Sarkin Hausawan Ibadan ba.
“Dakatarwar za ta ci gaba har zuwa lokacin da Majalsiar Al’ummar Arewa da ke Ibadan ta kammala nazarin lamarin,” in ji Sarkin Hausawan.