Rahotanni daga Legas na cewan sojoji da ’yan sanda sun isa gidan yarin da ke Ikoyi domin dakile yunkurin balla gidan yarin.
’Yan daba dauke da muggan makamai sun kai wa jami’an tsaro hari da nufin shiga gidan yarin.
Hadin gwiwar ’yan sanda da ma’aikatan gidan yarin sun yi ta musayar wuta da ‘yan daban da suka fara da kai wa mota mai sulke da ke aikin tsaro a wurin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya tababtar da harin da cewa, maharan “Sun isa kusa da wurin, muna kokarin fatattakar su”.
“An tura ’yan sandan kwantar da tarzoma domin tarwatsa su”, inji wani ganau.
Shaidu sun ce sun ga hayaki ya turnukowa daga harabar gidan yarin yayin da ake ta jin karar harbe-harbe a kusa da gidan yarin.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’a 48 bayan Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya ba da umarnin tura jami’an kwantar da tarzoma domin kara wa jami’an tsaro da ke aiki a gidajen yari karfi.
Idan za a iya tunawa a Gidan Yarin na Ikoyi ne ake tsare da wasu sojoji guda 50 da suka ki zuwa su yaki kungiyar Boko Haram.
Sojojin da ke tsaren sun sha yin roko ga Gwamnatin Tarayya ta yi musu afuwa kasancewar gwamantin ta fahimci cewa ba su da isassun kayan yakar kungiyar.