✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigimar Kwankwaso da Ganduje tana kawo wa Kano cikas — Mu’azu Magaji

Abin da ya fi alheri a yanzu shi ne Kwankwaso da Ganduje su jingine banbancinsu na siyasa.

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya bayyana damuwa matuka kan yadda ake ci gaba da samun karuwar rashin jituwa a tsakanin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Injiniya Mu’azu ya ce wannan rashin ‘yar ga-maciji da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje wadanda suka kasance masu rike da akalar siyasar Jihar na kara haifar da nakasun ci gaba da kuma zubar da mutuncin jihar gami da martabarta.

Tsohon Kwamishinan wanda a yanzu shi ne Shugaban Kwamitin Ayyukan samar da Bututun Iskar Gas a Jihar, ya ce muddin mutanen biyu suka ajiye banbancin akidarsy ta siyasa a gefe, to kuwa babu shakka “za a samu zaman lafiya mai dorewa da kuma daga martabar jihar a idon duniya.”

Cikin wasu jerin sakonni da tsohon Kwamishinan ya wallafa a kan shafinsa na Facebook, ya yi zargin cewa akwai wasu manyan ’yan siyasa a Jihar da ke goyon bayan wannan hamayya da kara rura wutar rashin jituwar da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje domin cimma wata manufa ta kashin kansu.

Ya kara da cewa idan har Kwankwaso da Ganduje za su fahimci irin barnar da rashin jituwarsa ke haifar wa a Kano, da sun ajiye sabaninsu a gefe domin wanzuwar ci gaba a Jihar.

A cewarsa, “A yanzu na fara fahimtar dalilin wasu ababen sharri da basa son Mai Girma Gwamna Ganduje ya sasanta da Kwankwaso don idan babu rikicin siyasa a Jihar, ba za su samu komai ba saboda rashin ilimi da ya yi musu lullubi. Ba su da wani aike da ya wuce su kai wa Gwamnan munafunci da ziga.”

“Abin da ya fi alheri a yanzu shi ne Kwankwaso da Ganduje su jingine banbancinsu na siyasa a gefe domin ci gaban Kano. Idan suka yi haka, to sun kare mutuncin kansu da kuma martabar Jihar Kano a matsayinsu na dattawanta,” inji shi.

Idan ba a manta ba, Mu’azu Magaji na daga cikin manyan magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya gabanin ya sauya sheka zuwa ta Gandujiyya ana gaf da gudanar da zaben 2019.

Aminiya ta samu cewa a ranar Lahadi ne Mu’azu Magaji ya kai wa Kwankwaso ziyara a gidansa da ke Abuja, inda ya jajanta tare da yi masa ta’aziyar rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso wanda ya rasu a karshen watan Dasumbar bara.