Kulob din Ribers United ta tafi kasar Sifen inda ta kai ziyara birnin Madrid don samun horo a kokarin tunkakar kakar wasa ta bana.
Kulob din ya bar kasar nan ne a ranar Talatar da ta wuce da misalin karfe 2 da minti 35 na rana daga filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Tun a ranar 1 ga watan Nuwamban wannan shekara da muke ciki ne kulob din ya fara yin atisaye don tunkarar kakar wasa mai zuwa. Kulob din ya samu nasarar lashe kofin Super 4 da aka yi a Enugu da hakan ta sa yake fatan zai haskaka a kakar wasa mai zuwa.
Wannan nasara da kulob din ya samu ce ta sa ya yanke shawarar tafiya Sifen don yin balaguro a birnin Madrid. Ana sa ran zai buga wasannin sada zumunta a can don karfafa wa ’yan kwallonsa gwiwa kafin ya dawo Najeriya.
Sannan idan suka dawo Najeriya za su zauna a Abuja na wadansu kwanaki kafin su zarce zuwa Kaduna don cigaba da samun horo kafin daga bisani su koma Fatakwal.
A ranar 15 ga watan Janairun 2017 ne ake sa ran za a fara gasar firimiyar Najeriya. A bara Enugu Rangers ce ta zama zakara a gasar a karon farko bayan shekara 32 rabonta da kofin.