✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Reece James zai yi jinya zuwa karshen kakar wasanni

Reece James ya sha fama da jinya a baya bayan nan.

Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Reece James ya tafi jinyar da ba zai dawo ba har sai wata kakar wasa.

James, wanda ya sha fama da jinya daban-daban, sau 16 Chelsea ta fara wasa da shi a kakar bana.

Wannan jinya ta baya-bayan nan na zuwa ne yayin karawar da Chelsea ta yi da Real Madrid a makon da ya gabata a Gasar Kofin Zakarun Turai.

Ko da yake, ya buga wasan har karshe, amma gwajin da aka masa bayan wasan ya fito da girman matsalar raunin na shi.

Kazalika, dan wasan kungiyar, Mason Mount shi mai yiwuwa ba zai sake buga wasa ba saboda tiyata da za a yi masa.