✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta sayi Eder Militao

Kungiyar Real Madrid, ta dauki mai tsaron baya na kulob din FC Porto, Eder Militao. Dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da…

Kungiyar Real Madrid, ta dauki mai tsaron baya na kulob din FC Porto, Eder Militao.

Dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da Zinedine Zidane ya saya, bayan da ya sake karbar aikin horar da kungiyar ta Real Madrid.

A sanarwar da Real Madrid ta sanar a shafinta na Intanet ta ce ‘’Real Madrid ta cimma yarjejeniya daukar dan wasan FC Porto, Eder Militao.”

Dan kwallon na Brazil ya amince zai koma Spain kan shekara shida, zai kuma koma can ne idan an kammala wasannin kakar bana.

Rahotanni sun ce kudin daukar dan kwallon Brazil din ya kai Fam miliyan 43.5, ana sa ran yarjejeniyarsa da Real Madrid za ta kare a karshen watan Yunin 2025.

Militao ya fara buga tamola a Sao Paulo daga nan ya koma FC Porto a watan Agustan bara, ya kuma taimaka wa kungiyar ta kasar Portugal ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta bana.

Tuni aka fitar da Real Madrid a gasar Zakarun Turai da kuma Copa del Rey, sannan tana ta uku a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya kamar yadda BBC ya ruwaito.