✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta kafa tarihin jefa kwallo 6000 a La Liga

kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ake wa lakabi da Los Blancos ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafa da suka ci kwallo 6000, inda…

kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ake wa lakabi da Los Blancos ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafa da suka ci kwallo 6000, inda ta zama kungiya ta farko a Spain da ta samu nasarar haka.

 A ranar Lahadin da ta gabata ce Madrid ta cimma nasarar haka bayan da Marco Asensio ya jefa kwallon da ta zama ta 6000, yayin da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema suka kara kwallaye a wasan da Madrid ta yi nasara a kan Betis da ci 5-3.

kungiyoyi biyar ne kawai a Turai suka ci kwallo 6000 a gasar rukuni da suke bugawa su ne Eberton da Arsenal da Liberpool da Aston billa da Manchester United, inda Eberton ke neman zama kungiyar da za ta jefa kwallo inda Eberton ke daf da jefa kwallo ta 7000.

An fara gasar cin kofin Spain ne a 1928/29, inda Real Madrid ta ci kwallon farko ta hannun Jaime Lazcano a karawar da ta yi da CE Europa. A fafatawar Real ta ci 5-0 kuma Lazcano ne ya ci hudu rus, tun daga nan sai da Madrid ta yi shekara 22 kafin ta saka sunanta cikin tarihin gasar La Liga.

A ranar 5 ga Nuwamban 1950 ne, Real ta ci kwallo ta 1,000 ta hannun Manuel Fernandez a karawarta da Athletic Club da aka tashi 5-2 a San Mames.

Paco Gento ne ya ci kwallo ta 2,000 a wasan da Real ta doke Pontebedra 3-1 a Santiago Bernabeu, a ranar 20 ga Janairun 1982, Real ta ci ta 3,000 ta hannun Juan Gomez a gumurzu da Salamanca.

Iban Zamorano ne ya ci kwallo ta 4,000 shi ne na biyun da ya ci a fafatawar da suka doke Real balladolid 5-0, yayin da Raul Gonzalez ne ya ci wa Madrid kwallo ta 4,500.

Guti ne ya ci ta 5,000 a ranar 14 ga Satumban 2008, a wasan da Real ta doke Numancia 4-3 a Bernabeu.

A kakar wasa ta 2012/13, Madrid ta hada kwallo ta 5,500 ta hannun Luka Modric a wasa da Malaga.