✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta dauki dan wasan bayan Chelsea Antonio Rudiger

Zai rika daukar albashin da ya kai Yuro miliyan 6.8 duk kakar wasa guda a Sfaniya.

Dan wasan bayan kungiyar Chelsea da ke buga gasar Firimiyar Ingila, Antonio Rudiger, ya rattaba hannu a kan kwantaragin kaka hudu da kungiyar Real Madrid mai buga gasar La Liga a Sfaniya.

Antonio Rudiger mai shekara 29 zai koma Real Madrid kyauta yayin da kwantaraginsa da Chelsea zai kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Jaridar wasannin kwallon kafa ta Goal ta ruwaito cewa dan wasan na kasar Jamus zai rika daukar albashin da ya kai Yuro miliyan 6.8 duk kakar wasa guda a Sfaniya.

Haka kuma bayanai sun ce bayan kulla yarjejeniyar, wakilin dan wasan, Sahr Senesie da kuma wani dan uwansa za su samu makudan kudi a matsayin tukwicin tabbatuwar kwantaragin da suka kai Dalar Amurka miliyan 37.

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne Real Madrid ta yarda za ta dauki mai tsaron bayan Chelsea, Antonio Rudiger a karshen kakar nan.

Wannan dai ya biyo bayan magiyar da kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya yi don ganin kungiyar ta dauko dan wasan.