✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ne kulob na farko a duniya

A jadawalin da Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta ftar, an nuna kulob xin Real Madrid na Sifen ne na farko bayan…

A jadawalin da Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta ftar, an nuna kulob xin Real Madrid na Sifen ne na farko bayan ya samu nasarar lashe gasar zakarun kulob na Turai sau uku a cikin shekara uku.

Wannan shi ne karo na huxu a jere da kulob xin yake rike da wannan kambu a jadawalin da hukumar ke fitarwa.

A jadawalin da Hukumar ta yi a ranar Litinin da ta wuce, an nuna Real Madrid ce ta farko, sai kulob xin Byern Munich na Jamus a matsayi na biyu sai FC Barcelona na Sifen a matsayi na 3 sai Atletico Madrid na Sifen a matsayi na 4 sai Jubentus ta Italiya a matsayi na 5.

Sauran sun haxa da kulob xin PSG na Faransa a matsayi na 6 sai Borussia Dortmund a matsayi na 7 sai Sebilla a matsayi na 8 sai Benfica a matsayi na 9 sai kuma Chelsea a matsayi na 10.

Haka kuma kulob xin Arsenal ne a matsayi na 11 sai Manchester City a matsayi na 12 sai FC Porto a matsayi na 13 sai Schalke 04 a matsayi na 14 sai kuma Manchester United a matsayi na 15.

Bayern Leberkusen na matsayi na 16 sai Napoli a matsayi na 17 sai Shaktar Donestsk a matsayi na 18 sai St Zenit a matsayi na 19 sai kuma kulob xin Tottenham da ke matsayi na 20.

Real Madrid ta samu wannan matsayi ne saboda irin manyan kofunan da ta lashe a ’yan shekarun nan.