✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwata a BBC – Umar karaye

Umar Yusuf karaye na daya daga cikin ma’aikatan BBC Landan da ya fara zama Mataimakin Shugaban Sashin Hausa na BBC. Shekara takwas da suka gabata…

Umar Yusuf karaye na daya daga cikin ma’aikatan BBC Landan da ya fara zama Mataimakin Shugaban Sashin Hausa na BBC. Shekara takwas da suka gabata ya bar aiki da gidan rediyon kuma Aminiya ta zanta da shi, inda ya bayyana yadda ya fara aikin da dalilin ajiye aikin bayan ya shafe shekara ashirin:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

Umar karaye: Sunana Umar Yusuf karaye, an haife ni a garin karaye a Jihar Kano ranar 16 ga Yunin 1956. Na yi firamare a 1964 a karaye na tafi makarantar Middil ta Gwarzo a 1968 zuwa 1970, a can na ci gaba da sakandare daga 1971 zuwa 1975, sai Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Sakkwato, na yi Jami’ar Bayero, Kano a 1978, mu ne na farko da aka fara koyar mana aikin jarida a jami’ar, na gama a 1981. Na yi hidimar kasa a gidan talabijin na NTA Maiduguri, daga 1981 zuwa 1982. Na kama aiki da kamfanin buga jaridun Triumph na Kano a 1982, aka tura ni Maiduguri a matsayin wakili har zuwa 1983, inda aka dawo da ni Kano. Na ci gaba da aiki a wurin har zuwa 1986. Marigayi Alhaji Abubakar Rimi (Allah Ya jikansa) shi ya bude kamfanin jaridar Triumph, Malam Haruna Adamu shi ne Manaja Darakta na farko, Mista Clement Isaiah, mahaifin Mista Sam Nda Isaiah, Manajan Editanmu, Malam Rufa’i Ibrahim, Editan Triumph, akwai takwararta ta Hausa, Albishir da ta Hausar Ajami, Alfijir. Da marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo, (Allah Ya jikansa) ya karbi mulki, sai aka dauki ma’aikatan wurin a matsayin daukar Rimi. Duk wanda ya zo neman aiki a sabuwar gwamnati, sai a turo shi kamfanin jaridun Triumph, har ya zamo sai ka nemi wurin zama a dakin labarai ka rasa saboda yawan ma’aikata. Mutane sun zo ba su ma san mene ne aikin jaridar ba da sauransu, sai ya zama idan aka tashi aiki a yini ba a kore ka ba, to, ka ji dadi, haka aka yi ta aiki cikin firgici. Ana cikin wannan hali sai wani abokina mai suna Muhammad Dada da ke aiki a BBC ya zo gida hutu, muna hira sai na yi masa bayanin irin zaman da muke ciki, sai ya ce to ka taho BBC mana. Sai na ce ni ban taba tunanin zuwa BBC ba, sai ya ce ai ba wani abu in ya koma zai aiko mani da fom.
Aminiya: To dama kai wane bangare ka fi sha’awa a bangarori uku na aikin jarida?
Umar karaye: Duka bangarorin ukun ana koyar da su a jami’a, sai dai zabi ya rage na mutum, idan kai ma’abocin rubuce-rubuce ne, to bangaren jarida irin wannan jarida taku ta Aminiya za tafi dacewa da kai. In ko bangaren rediyo ko talabijin ne akwai abubuwan da ake bukatar ka samu. Ni na hada duka kasancewar duka bangarori ukun na yi aiki a cikinsu, amma dai na fi jin dadin aikin rediyo a lokacin da na yi aiki a BBC. To bayan ya aiko mini da fom a 1984, sai na cika, to amma sai a 1986, sannan na tafi na fara aiki da su a watan Afrilu.
Zuwana BBC da farko an dauke ni a matsayin kwantaragi na shekara 4 da wata 3, daga kanmu aka fara, kuma ba a sabunta shi, kafin haka suna ba da aikin ne na shekara uku ba sabuntawa, to amma daga kanmu sai suka ce sun sauya zuwa shekara 4 ba kari. Shekarata biyu da su sai suka sauya min takarda zuwa ma’aikacin dindindin, da ke da fansho da sauran abubuwa, muka share wuri muka zauna sai abin da hali ya yi. Sai dai ka san komai ya yi farko zai yi karshe, a shekara ta 2006 sai na ajiye aiki bayan na shekara 20 a wurin.
Aminiya: Wadanne abubuwa suka burge ka a yayin zamanka a BBC da ba za ka manta da su ba?
Umar karaye: Suna da yawa, wasu zan iya tunawa, wasu ba zan iya ba, amma muhimmi daga ciki shi ne, lokacin da aka tabbatar da ni a matsayin cikakken ma’aikaci, maimakon kwantaragi. Yadda abin ya faru shi ne, a lokutan bukukuwan Sallah akan yi shirin gaishe-gaishe, to, da wata Sallah ta zo sai na samu shugaban sashin Hausa na lokacin wato Barry Barges na ce da shi, amma wannan shiri na zabi sonka da ake yi, ina son na sauya shi zuwa shiri na musamman da za a bugo waya daga garuruwan Hausa da sauran duniyar Musulmi, a yi bayanin yadda bikin Sallah ke gudana a wuraren. Kasancewar lokacin mun fara samun wakilai na kanmu a sashin Hausa, har shugaban jaridarku Malam Kabir Yusuf yana Zimbabwe yana aiko mana da rahoto, kamar yadda ya yi a Afirka ta Kudu da kuma Legas a baya. To abin zai yiwu ba zai yiwu ba, wata rana an zo taron jagororin gidan wanda ya zo daidai da lokacin da muke gabatar da shirin karfe 2:45 na rana. Ban mancewa ni da Adamu Aliyu Kiyawa ne, muna cikin sutodiyo, mu tuntubi wakilinmu na wannan gari mu tuntubi na wancan, mu tambaye su yadda bikin Sallah ke gudana a can, har dai a ka zo kan Harare kasar Zimbabwe inda Kabiru Yusuf ya aiko mana hade da Kiran Sallah. To a yayin zaman sai shi shuguban namu Barry Barges, ya gabatar da al’amarin ga jagororin har ya bukaci su dan saurara don jin yadda shirin ke gudana. Sai shirin ya bai wa shugabannin sha’awa, suka tambayi Barry Barges, wane ne ya tsara shirin, ya gaya musu Editan Shirye-Shirye ne na riko. Sai suka ce me kake nufi da na riko, kawai a tabbatar da shi, to, shi ke nan muna fitowa daga sutodiyo sai ga Barry da fayel, ya kira ni ya ce an tabbatar min da matsayin. To wannan na daya daga cikin abubuwan da suka yi min dadi da ba zan manta da su a zamana na BBC ba. Abu ne kamar kasada in ya yi kyau, ka ji dadi in akasin haka ne, kai ne da laifin, wanna ba karamin abin farin ciki ba ne. Haka akwai daukar wakilai da ke aiko da rahotanni, duk a lokacinmu ne muka ba da shawara aka tabbatar da shi, saboda a baya sai dai a fassara abin da wakilai Turawa suka turo kadai. Haka ba ni mancewa da lokacin da aka ba mu wata uku, wato shugaba Barry Barges da mataimakinsa da ni, na mu bullo da shirye-shirye da tsare-tsaren da za su inganta sashin Hausa, a lokacin ne muka kawo batun wakilai. To wadannan a bangare abubuwa masu dadadawa ke nan. Idan muka koma daya bangaren, babban abin da ya ba ni takaici da ba zan manta da shi ba, shi ne wata Asabar da nake da aikin rana, sai na kuskure ban zo ba. Yadda al’amarin faru shi ne, bayan na gabatar da shiri a ranar Juma’a, sai na zo na duba takardar jerin sunayen masu gabatar da shiri, sai na dauka ranar Lahadi ce zuwana na gaba, ashe kashegari Asabar ce da rana, to haka lokacin shirin ya wuce ba tare da an gabatar da shi ba, in ban da faifayin ko- ta-kwana da aka yi ta sawa. Barry ya bugo mini waya ya ce lafiya, na ce lafiya, ya ce kana ina, na ce ina gida mana, to a nan ne ya ankarar da ni, ai duk da dai lokaci ya riga ya wuce haka na taso har yake ce mini in kana ganin abin ya saka firgici, ka hakura da gabatar da shirin yamma a sa wani, sai na ce zan iya, na kuma gabatar da shirin na yamma. To wannan abin na daga cikin abubuwan da ba zan manta ba a zamana na BBC.
Aminiya: Wane ne ya fara shugabantar sashin Hausa a bayan Turawa?
Umar karaye: Abin da suka fara da shi a lokacin shi ne Mataimakin Shugaba na karba-karba da ake dauka daga cikin manyan Editocin Shirye-Shirye hudu, ana kuma ba da mukamin ne na tsawon wata uku, an fara da ni, sai Isa Abba Adamu, sai Abubakar Kabir Matazu, sai Jamila Tangaza. To amma bayan an sallami Barry, sai aka zo aka yi hukuma (board), aka bai wa kowa damar neman shugabancin sashin, kuma bayan haka ne aka bai wa Isa Abba Adamu matsayin cikakken shugaban sashin Hausa na farko daga cikin Hausawa, bayansa sai Jamila Tangaza, sai kuma Mansur Liman a yanzu.
Aminiya: Yaya za ka bayyana bambancin yanayin aiki a BBC, jiya da yau?
Umar karaye: Akwai bambanci musamman a bangaren ci gaba da kuma saukin aiki, a lokacin da muka je, ana amfani ne da keken rubutu irin wanda za ka yi ta bugawa ba kwamfuta ba. Ni lokacin da na je ma da hannu nake rubutuna, daga baya ne na fara da tafureta, ana nan sai aka koma tafureta mai aiki da lantarki, har aka zo irin ta yanzu wadda komai kake yi za ka gani a kwamfuta, idan da gyara ka yi kafin bugawa, wanda muke kira “cool editing.” Yanzu ga shi kusan komai a nan Abuja ake yi. To irin wadannan sauye-sauye, na daga cikin abubuwan da suka sa muka yi shawarar ajiye aiki ni da Usman Muhammed, ba don lokacin ritayarmu ya yi ba. Da muka ga canje-canjen suna yawa, muka ce, kai tun muna cewa wannan abin na da wuyar koya, kada a zo lokacin da za a bukaci mu yi abu ya gagare mu, gara mu bar wa yara su ci gaba da aikin, tunda su sun zo da ilimin abin, maimakon a zo a ji kunya.
Aminiya: Yaya abokan aiki da kuka bari, ko kuna haduwa a yanzu?
Umar karaye: Yakan dade ba mu hadu ba, musamman kamar Usman Muhammed tunda muka bar BBC a 2006, ban sake ganinsa ba, kuma ba mu sake yin ko waya ba, sannan ban san inda yake ba. Sai dai Adamu Kiyawa tunda shi a Kano yake ina jin labarinsa, kowa hidimarsa ta yi yawa. Irin su Salisu Na-Inna dambatta, su Ibrahim Salisu Yakasai da Abubakar Kabir Matazu, su Jamila Tangaza, tunda su muna tare a nan Abuja, to ko ba mu hadu ba ma dai, muna yin waya da juna.
Aminiya: Kasancewar ka shekara wajen ashirin a can, yaya kake jin yanayin zama a nan Najeriya?
Umar karaye: To a can dai a lokacin da muka je akwai yarinta, mutum yana da shekara ashirin da ’yan kai, abubuwa suna da sauki kuma sun sha bamban, al’ada daban, ka dau wasu da ka ga za ka iya yi, wadanda ba su dace da naka ba ka bari. Amma ba wani sauyi saboda kowa ya tafi da iyalinsa, ’ya’yana duk a can aka haife su, domin na yi aure a 1985, muka tafi Landan a 1986, dana na farko Sadik a can aka haife shi, mai bi masa Muhammed, sai ta karshe Hauwa duk a can aka haife su, kuma har yanzu can suke makaranta, suna tare da matana, su ’yan kasa ne a can, haka ni ma dan kasa ne a can kamar a nan, in na je can na yi amfani da fasfo na Ingila, in na dawo nan na yi amfani da na Najeriya.
Aminiya: Me kake yi yanzu a nan Najeriya?
Umar karaye: Kamar yadda ka gani nan ofishinmu ne, wato Global Resources Limited, muna abubuwan da suka danganci al’amuran rediyo da talabijin, ma’ana ba a bar aikin gaba daya ba, muna yin tallace-tallace a rediyo da talabijin, kuma muna shirya horo ga manyan ma’aikatan gwamnati da kamfanoni a kwararru a fannin tuntuba, a basu horo a Dubai ko a Ingila da sauransu.
Aminiya: Akwai wani mai gabatar da shiri a Rediyon Najeriya na Kaduna a shekarun baya mai suna Shehu Yusuf karaye, ko dan uwanka ne.
Umar karaye: Allah Sarki, Allah Ya jikansa ya dade da rasuwa, koda na ke Landan an sha yi mini tambaya a kan wannan. A gaskiya ba wata dangantaka ta jini a tsakaninmu, sai dai ta addini da kuma gari, kuma sunan iyeyenmu ya zo daya, na san shi sosai, saboda abokin ajin wana ne tare suka yi karatu.
Aminiya: Yaya batun iyaye ko kuna tare?
Umar karaye: Mahaifina ya rasu a 1998 a lokacin na zo hutu na samu bai da lafiya, har hutun ya kare na nemi kari, ba a yi mako ba, sai Allah Ya yi masa cikawa, mun je asibiti likita ya ce ba wani magani tsufa ce kawai, ya rasu bai ji bai gani kusan komai na jikinsa ya daina aiki, amma dai mahaifaya tana raye.