Masu iya magana sun ce, ‘Kada Allah Ya kawo ranar yabo.’ Wannan kalami shi ya fara zuwa raina, bayan da aka sanar da rasuwar Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Hakan ta kara bayyana bayan da jama’a daban-daban suka yi ta nuna alhini tare da fadin kyawawan halayensa da ayyukansa, kamar yadda aka yi ta nanata irin kwazonsa da ayyukansa da irin rashin da aka yi nasa. Alhali kuwa lokacin da yake raye, ya kasance jami’in Gwamnatin Buhari da aka fi tsangwama.
Malam Abba Kyari ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta gabata (17-04- 2020), sanadiyyar cutar Kurona da ya yi jinyarta a Legas. Shi ne babban jami’in gwamnati na farko da ya rasu sanadiyyar wannan cuta ta Kurona a Najeriya.
- Yadda ake tururuwa zuwa gidan Abba Kyari a Maiduguri
- Yadda gidan Abba Kyari na Kaduna ya kasance
- An tube kwamishina a Kano don murnar rasuwar Abba Kyari
Shugaba Buhari ne ya nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadarsa a watan Agustan shekarar 2015.
Marigayin ya dawo Najeriya a ranar 14 ga Maris, 2020 daga Jamus, inda ya je aikin kammala yarjejeniya da Kamfanin Siemens, wanda zai yi aikin inganta wutar lantarki a Najeriya. Bayan ya yi gwajin cutar Kurona ne, sai a ranar 24 ga Maris da ya gabata aka tabbatar masa da cewa yana dauke da cutar.
Kalamansa na karshe ga al’umma sun bayyana ne ta hanyar wata wasika da ya fitar a ranar 29 ga Maris, 2020, inda ya ce: “Na rubuto wasikar nan ce da nufin sanar da ku cewa, sakamakon shawarar likitoci, zan kaura zuwa Legas a yau domin a ci gaba da yi mini wasu gwaje-gwaje da kula da lafiyata. Wannan mataki na dauke shi ne domin kariya, domin kuwa ni dai ina jin lafiya da karfin jiki amma a makon jiya aka yi mini gwaji kuma aka tabbatar mini da cewa ina dauke da cutar Kurona, cutar da ke karade duniya. Ni dai na bi dukkan sharuddan da gwamnati ta tanadar na cewa a killace mai dauke da wannan cuta.”
Ya kara da cewa shi da kansa ya shirya amfani da dukiyarsa domin kula da kansa, kasancewar kamar an yi wa gwamnati yawa. “Kamar wadansu da dama da aka yi wa tes kuma suka kasance suna da kawayar cutar, ni dai ban taba jin wani zazzabi ko wani laulayi da ake alakantawa da mai cutar ba kuma na ci gaba da aikina daga gida. Ina fata nan ba da jimawa ba zan dawo bakin aikina.”
Wanene Abba Kyari?
An haifi Malam Abba Kyari ne shekara 67 da suka gabata a Maiduguri, Jihar Borno. Ya yi karatunsa na farko a Maiduguri da kuma Wusasa, Zariya Jihar Kaduna, inda daga bisani kasancewarsa dalibi mai kwazo ya samu gurbin zurfafa karatu a Ingila. Ya samu digirin farko a Nazarin Halayyar Dan Adam (Sociology) a Jami’ar Warwick da kuma wani digirin a fannin Shari’a (Law) a Jami’ar Cambridge. Ya halarci Makarantar Kwarewa a Aikin Lauya ta Najeriya a Legas, a 1983. Ya halarci manya da matsakaita da kananan kwasa-kwasan ilimi iri daban-daban a kasar Switzerland da Amurka.
A fannin aiki kuwa, marigayin ya taba aiki a matsayin dan rahoto a jaridar New Nigerian a 1970, sannan ya taba rike mukamin Editan jaridar The Democrat a Kaduna. A fannin aikin Lauya kuwa, ya taba aiki da kamfanin aikin Lauya na Fani- Kayode da na Sowemimo.
Ya yi aiki a bankuna daban-daban da suka hada da Bankin AIB, kuma ya
taba zama Manajan Darakta a Bankin UBA. A 1990, ya rike mukamin Kwamishinan Lafiyar Dabbobi da Gandun Daji a Jihar Borno. Daga karshe, ya kasance Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tun daga 2015 zuwa rasuwarsa a Juma’ar da ta gabata.
Sakonnin ta’aziyya daga gida da waje:
Bayan rasuwarsa, mutane daban- daban da suka hada da shugabannin kasa, gwamnoni da muhimman mutane daga gida da waje sun yi ta bayyana sakonnin alhini game da marigayin, inda suka bayyana shi da mutumin kirki, jajirtacce kuma mai gaskiya.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin dan Najeriya na gaskiya, mai kishin kasa kuma aboki mai biyayya da amana. Ya ce ya yi mu’amala da shi ta tsawon shekara 42.
“(Marigayi Abba) ya kasance mafi kokari da gaskiya daga cikinmu, wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin daukakawa da bunkasar Najeriya,” inji Shugaba Buhari.
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ma ya bayyana ta’aziyyarsa da ta matarsa Dolapo Osinbajo, inda suka yi addu’ar Allah Ya jikansa da gafara.
Haka shi ma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana rasuwar Abba Kyari da babbar shaidar da ke nuna cewa cutar Kurona gaskiya ce. “Akwai manyan darussa da za a fahimta daga rasuwar Abba Kyari, daya daga cikinsu shi ne, wannan cuta gaskiya ce. Dalili ke nan nake kara natata cewa lallai ne kada mu yi wasa da ita,” inji shi. Shi ma ya roki Allah Ya yafe wa marigayin.
Shugabannin kasashe daban- daban sun aiko da sakonnin ta’aziyya ga Shugaba Muhammadu Buhari. Wadansu daga cikinsu sun hada da Shugaban Kasar Ghana, Nana Akuffo-Ado da na Nijar, Muhammadou Youssofou da tsohon Shugaban Jamhuriyar Benin, Yayi Boni da tsofaffin shugabannin kasa Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar. Haka gwamnoni daban- daban da hamshakan ’yan siyasa da sarakunan gargajiya da malaman addini da manyan ’yan kasuwa maza da mata duk sun yi ta’aziyyar marigayin.
Marigayi Abba Kyari ya kasance mai gudanar da ayyukan jinkai da tallafin marasa galihu a boye. Wadannan halaye nasa sun fito fili bayan rasuwarsa. A yayin ta’aziyyarsa, Shugaban Kungiyar Bunkasa Yankin Bama, Dokta Ali Bakari Muhammad, ya bayyana marigayin da mutum mai tausayi da gudanar da ayyukan jinkai. Wani mai gudanar da wata makaranta mai zaman kanta mai suna Future Prowess, Barista Zanna Mustapha, ya ce marigayin ne ya dauki nauyin marayu 150 da suka rasa iyayensu a rikicin Boko Haram a Jihar Borno, duk da cewa ya yi masa kashedi cewa kada ya fada wa kowa.
“Shi ke daukar nauyin marayu 150 tun daga shekarar 2015 har zuwa yau. Kuma ya gargade mu cewa kada mu sake mu sanar da wannan abin kirki nasa,” inji shi.
Kungiyoyi daban-daban da suka hada da IPI da MURIC (Kungiyar Musulunci) da CAN (ta Kiristocin Najeriya) da Shugaban Bankin Bunkasa Afirka (AfDB), Adesina duk sun yi ta’aziyyar. Haka Etsu Nupe da Bashir Othman Tofa da Geoffrey Onyeama, Ministan Al’amuran Kasashen Waje da Gwamnatin Jihar Kaduna da Ministan Abuja.
Ita kuwa Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Yamma, shafuka ta saya a manyan jaridun kasar nan tana ta’aziyya tare da fadin kyawawan kalamai game da marigayin. Shi ma Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa, rubutu ya yi na musamman domin ta’aziyya a jaridar Daily Trust, kamar yadda Farfesa Iyorwuese Hagher, tsohon Minista a Ma’aikatar Makamashi da Karafa ya yi.
Hatta babban mai sukar gwamnatin Buhari Femi Fani- Kayode ya bayyana kyawawan halayen marigayin/ Allah Ya jikansa da rahma, amin!
- Yadda ake tururuwa zuwa gidan Abba Kyari a Maiduguri
- Yadda gidan Abba Kyari na Kaduna ya kasance
- An tube kwamishina a Kano don murnar rasuwar Abba Kyari