Fursunoni sun rungumi ayyukan badala a tsakaninsu sakamakon rashin hasken lantarki na tsawon makonni a gidajen gyaran hali na Jihar Yobe.
Kamar yadda wata majiya ta bayyana, hatta matsugunan jami’an gidan gyaran halin da na sauran jami’an tsaron da ke harabar sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon katse hasken lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Yola (YEDC) ya yi.
- Matar da likitoci suka manta almakashi a cikinta tsawon shekara biyar
- Sankarau ta kashe mutum 118 a jihohi 22 na Najeriya —NCDC
Aminiya ta ruwaito cewa, matsalar rashin wuta da aka shafe tsawon makonni 3 ana fama da ita, ta janyo ana aikata ayyukan na assha da suka hada da yawaitar luwadi da madigo a tsakankanin fursunonin.
Haka kuma rashin wutar ya janyo an dakatar da sana’o’i da dama da ke dogaro da wutar lantarki a wuraren da ma’aikatan gidan gyaran halin ke zama.
Wasu jami’an gidan gyara halin ka da suka yi magana da manema labarai tare da tabbatar an sakaya sunansu, sun yi tir da halin da aka tsinci kai na karuwar ayyukan badala a tsakanin fursunonin.
Haka kuma, sun koka da yadda hukumar da abin ya shafa ke ci gaba da kin maido da hasken wutar lantarki wanda a cewarsu hakan ke kara ta’azzara lamarin.
Sun yi kira ga mahukuntan da abin ya shafa kan cewa lallai akwai bukatar a gaggauta shawo kan matsalar.
Kazalika, jami’an sun bayyana yadda suka yi karo-karo na Naira 2,000 domin hada gudunmuwar da aka bai wa wani jami’in hukumar ta YEDC don a samu saukin lamarin.
“Hasken lantarki na gidan ma’aikata da farfajiyar gidan yarin sun bambanta amma daga baya sai hasken farfajiyar ya katse aka hada shi da na ma’aikatan.
“A yanzu muna cikin duhu kusan kwanaki 21.
“Kamar yadda muke magana da ku yanzu, babu haske a farfajiyar gidan yarin gaba daya kuma akwai cunkuson gaske a matsugunin fursunoni mata wadda hakan ya janyo mana wannan mummunar barazana ta aikata badala tsakaninsu.
“Katse hasken wutar lantarki ya taimaka wajen habaka ayyukan luwadi da madigo a tsakanin fursunonin kamar yadda aka ambata a baya.
“Babu wani hasken da zai taimaka akan harkokin tsaro a cikin farfajiyar gidan yarin kuma muna da injin janareta wanda zai mamaye gaba dayan gidan gyaran hali, amma ba a yi amfani da shi ba tsawon shekaru 6 da suka gabata kamar yadda muke magana da ku.
“Abin da kawai janareta ke bukata don fara aiki yadda ya kamata shi ne batir da mai (Diesel),” in ji jami’an.
Jami’an kula da gidan kason sun roki a ba su kulawar gaggawa don magance matsalolin da suke fuskanta hade da fursunonin.
Kokarin zantawa da Manajan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Yola Rukunin Kasuwancin Damaturu ya ci tura, inda ya ce ya tafi hutun Sallah.
Aminiya ta samu rahoto daga wata majiya da ba a bayyana ba daga kamfanin rarraba wutar na Yola a Damaturu, tana mai cewa akwai yarjejeniya tsakanin kamfanin da jami’an tsaro na gidan gyaran halin.
Ya ce, “Sun yi alkawarin sasantawa a watan Maris na bana amma sun kasa cika alkawarin da suka yi da su wanda hakan ne ya kai ga katse wutar lantarki a duk fadin gidajen na gyara hali a garuruwan Potiskum, Nguru da Gashua duk a Jihar Yobe.”