Shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana a gaban babban zauren Majalisar Tarayya domin yin bayani game da matsalar tsaro da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Shafukan Zumuta, Lauretta Onochie ta sanar da yammacin ranar Litinin cewa Buhari zai amsa gayyatar majalisar a ranar Alhamis, 10 ga Disamba, 2020.
Buhari zai yi wa Majalisar bayani ne bayan ta bukaci hakan gabanta bayan kisan gillar da kungiyar Boko Haram ta yi wa manoman shinkafa a garin Zabarmari na Jihar Borno.
Yankan ragon da kungiyar ta yi wa manoma ya fusata ‘yan Najeirya, musamman bayan da hadimin Buhari kan yada labarai, Garba Shehu ya ce manoman ba su da izini daga sojoji na fara harkokin noma a yankin.
Kisan gillar ta kara taso da ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya da kiran Shugaban Kasar da ya kori Manyan Hafsoshin Tsaro.