✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin Tsaro: An kama masu zanga-zanga 43 a Katsina

A ranar Talata Rundunar ’Yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ta cafke akalla mutum 43 da suka fito zanga-zangar nuna bacin rai a kan tabarbarewar…

A ranar Talata Rundunar ’Yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ta cafke akalla mutum 43 da suka fito zanga-zangar nuna bacin rai a kan tabarbarewar tsaro a yankin Karamar Hukumar Jibia ta jihar.

Kakakin ’Yan Sandan na Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ba da shaidar hakan yayin zanta wa da manema labarai ya na cewa barnar da masu zanga-zangar suka haddasa a yankin ta sanya aka dasa wawa a kansu.

Ya ce an kama mutanen ne a garin Daddara da ke karamar Hukumar ta Jibia sannan kuma an gano wata gawa daya da a yanzu ake bincike a kai.

Sai dai masu zanga-zangar sun ikirarin cewa jami’an ’Yan sandan da ke kokarin hana su bayyana fushi na da alhakin kashe daya daga cikin jama’arsu tare da gadar wa da dama daga cikinsu raunuka iri-iri.

Masu zanga-zangar sun bankawa wani ofishin ‘Yan Sandan wuta a kauyen na Daddara domin nuna bacin ransu dangane da tabarbarewar rashin tsaro musamman yadda ta’adar masu garkuwa da mutane da ’yan daban daji ta zama ruwan dare.