Babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta yi watsi da karar farko da lauyan mijin Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ya shigar, yana kalubalantar hurumin sauraran karar raba aurensu.
Balaraba Ganduje ce dai ta shigar da karar mijin nata, Inuwa Uba, ta hannun lauyanta, Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa, tana rokon kotun ta raba aurensu ta hanyar Khul’i, saboda ta gaji da zama da shi.
- Bayan wata 11, farashin kayayyaki ya sauka a karshen 2022 a Najeriya – NBS
- Kotu ta yanke wa mutum 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun
Ta kuma bukaci kotun ta ba ta damar biyansa sadakinsa na N50,000 da ya biya lokacin aurensu.
Sai dai lauyan mai gidan nata, Barista Umar, ya ce bai san nawa ne sadakin ba, daga nan ne kuma Alkalin ya ba wa bangarorin biyu umarnin komawa su tabbatar daga ma’auratan.
Da yake ganawa da manema labarai bayan zaman kotun, lauyan mijin Balaraba, Barista Umar ya ce zancen ya wuce maganar dawo da sadaki, domin wanda yake karewa na da sharudda game da wasu abubuwa da ya mallaka, bayan maganar sadakin.
Sai dai ya ce a shirye suke su yi sulhu da diyar Gwamnan.
Alkalin kotun, Halliru Abdullahi, ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Janairu don jin ainihin kudin sadakin.