✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin masana’antu ne matsalar matasa a Najeriya -Sarkin Wandi

An bayyana rashin wadatar masana’antu kowace kusurwa ta Najeriya a matsayin babbar matsalar da ke barazana ga rayuwawar matasa, lamarin da ke sa karuwar masu…

Sarkin Wandi, Alhaji Mohammed Bello Manda AliyuAn bayyana rashin wadatar masana’antu kowace kusurwa ta Najeriya a matsayin babbar matsalar da ke barazana ga rayuwawar matasa, lamarin da ke sa karuwar masu zaman kashe wando ba tare da samun ayyukan yi ba.
Sarkin Wandi, a karamar Hukumar Dass, Alhaji Mohammed Bello Manda Aliyu, ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a Bauchi, inda ya ce matukar ana son shawo kan matsalar tsaro da rashin aiki yi, dole sai gwamnatoci sun hada kai da masu hannu da shuni an saukaka hanyoyin kirkiro da manya da kananan masana’antu, tare da farfado wadanda suka durkushe.
Alhaji Bello ya ce duk tallafin da ake bayarwa na Naira dubu biyar ko goma ga matasa ba zai samar da mafita ba, saboda idan suka kashe su, za su koma ba wajen zuwa, ba hanyar samun wasu kudin, daga karshe sai shaidan ya zama abokin shawararsu. Daga nan sai jin haushin masu mulki da ’yan siyasa da duk wani mai abin hannu. Matsala kadan, idan ta taso, sai matasan su dauki doka a hannunsu. Wasu kuma su rika tare mutane suna amshe musu dukiya ko neman hanyoyin tayar da hankulan jama’a a kan abin da bai kai ya kawo ba.
Ya shawarci shugabanni su sake tsarin hanyar samar da ayyukan yi ga matasa. “A fitar da kudi a raba wa ’yan kasuwa da manoma, tsakani da Allah, ta yadda za su gina kamfanoni manya da kanana da gonakin noma da kiwo, don a samu karuwar ayyukan yi, a rage yawan matasa masu zaman kashe wando. Duk abin da za ka ba matashi, idan ba ka samar da wajen da zai zauna na tsawon awoyi a wuni ba, to shaidan ne zai kasance abokin shawararsa.
Ya bukaci iyaye su karfafa tarbiyyar yaransu, su rika sanin me ’ya’yansu ke yi don gudanar da rayuwa.
Ya shawarci ’yan siyasa su daina amfani da matasa wajen banga da neman tayar da hankulan mutane saboda wasu muradu na kai ko neman matsayi don a samu ciyar da kasa gaba da gina al’umma.