Yanzu haka dai sarauniya Elizabeth ta Ingila, mai shekaru 96, na kwance a gidan sarautar kasar na Balmoral Castle tana fama da rashin lafiya.
Jaridar New York Times ta rawaito cewa rashin lafiyarta ta na kara tsananta, wanda ya tilasta fid da sanarwar halin da take ciki.
- Sojoji sun kama mai tattara wa Boko Haram bayanai a tsakiyar Abuja
- Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP ya yi murabus
Elizabeth da ta shafe shekaru 70 tana mulkin kasar, ta soke wata tattaunawa ta yanar gizo da aka tsara za ta yi da ‘yan Majalisar Dokokin Kasar ranar Laraba, saboda shawarar da likitoci suka bata ta samun hutu.
Sai dai hakan ya janyo ce-ce-ku-ce, bayan an ga wata mataimakiya ta musamman ta rada wa Firaminista Lizz Truss wata magana a kunne, daga nan ta mike cike da fargaba ta bar zauren majalisar ba tare da bata lokaci ba.
Kamar yadda yake a al’adar Ingila, Sarauniyar ta gayyaci Liz Truss don kafa sabuwar gwamnati, matakin da ya ke nuna mika mulki gare shi a hukumance daga hannun Boris Johnson.
Boris Johnson dai ya mika takardar murabus ga sarauniyar sa’a daya kafin hakan, kuma an maida duka tarurrukan biyu daga Fadar Buckingham zuwa Balmoral don hutar da Sarauniyar zuwa birnin Landan.
Ya zuwa lokacin hada rahoton dai babu cikakken bayanin yanayin rashin lafiyar Sarauniyar ba, sai dai fadar ta fada a baya cewa tana fama da matsalolin motsi.
Haka kuma sanarwar ta ce duk da ta warke sarai daga cutar Covid-19 a watan Fabrairu, har yanzu ba ta murmure sosai ba.