✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin kudi ne babbar matsalar FOMWAN- Barista Hannatu

Barista Hannatu Muhammad Kabir wata  babbar lauya ce a Hukumar Shari’a da ke garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa, kuma ita ce Shugabar kungiyar Mata…

Barista Hannatu Muhammad Kabir wata  babbar lauya ce a Hukumar Shari’a da ke garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa, kuma ita ce Shugabar kungiyar Mata Musulmi ta (FOMWAN) reshen jihar. A zantawarta da Aminiya, ta bayyana kokarin da kungiyarsu take yi wajen kare hakkin mata Musulmi da nasarorin da ta samu da kalubalen da take fuskanta da kuma sauran batuttuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ki gabatar da kanki?
Barista Hannatu: Sunana Barista Hannatu Muhammad Kabir. Lauya kuma shugabar  Hadadziyar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen jihar Nasarawa.  kungiyar kamar lema ce ta sauran kungiyoyin mata musulmi kamar su kungiyar ’Yan uwa matan musulmi da kungiyar Lauyoyi Mata Musulmi da sauransu, duka suna karkashin FOMWAN ne. Kuma babban aikinmu duka shi ne kare hakkin mata Musulmi,musamman ma matan aure.
Aminiya: Akwai lokacin da kuka gudanar da wata zanga-zanga kwanakin baya a Lafiya. Me ye ya yi zafi?  
Barista Hannatu: Dalilin zanga-zangar shi ne mu nuna bakin cikinmu dangane da sace yara ’yan mata kimanin 300 da ’yan kungiyar Boko Haram suka yi a garin Chibok da ke jihar Barno. Wannan ya sa muka fito zanga-zanga don mu nuna wa gwamnati bakin cikinmu mu kuma nuna mata ba mu yarda da tafiyar hawainiyyar da ake wajen  ceto su. Idan ka lura lokacin macin munsa bakaken tufafi tare da takwarunmu mabiya addinin Kirista karkashin kungiyar Kiristoci ta CAN.
Aminiya: Me kungiyarku ke yi don ganin an biya matan jami’an tsaro musulmi da ’yan kungiyar Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo kwanakin baya a jihar Nasarawa?
Barista Hannatu: Ba shakka akwai matan jami’an tsaro musulmi da dama da wancan kisan Alakyo ya shafa. Kamar yadda na bayyana maka a baya babban aikin kungiyarmu shine kare hakin mata musulmi a duk lokaci da damuwa irin wannan ta taso. Lokacin da lamarin ya auku ba mu tsaya cewa sai matan musulmai kawai zamu taimakawa ba don mace mace ce ko da ko wane irin addini take bi, har in an shiga hakkinta muna kokari mu karbo mata. Abu na farko da muka yi shi ne bayan mun je mun jajanta musu a gidajensu mun kwantar masu da hankali. Sai muka dawo muka je gurin gwamnati muka bayyana mata cewa matan nan ya dace a taimaka musu. Daga nan sai Uwargidan Gwamnan Jihar nan Salamatu Tanko Al Makura wadda dama ta san da zamanmu ta kuma san mahimmancinmu ta ba su gudummuwar kayayyakin abinci da kudi da sauransu.  Mu kuma muka hada kai a kungiyance da takwarorinmu matan kungiyar CAN, muka ba su namu tallafin da suka kumshi kayan abinci da tufafi da kayayyakin yara da sauransu. Har ila yau mun nema masu tallafi daga gun matan gwamnonin jihohi da ke makwabtaka da mu, inda Uwargidan Gwamnan jihar Neja da ta Binuwai suka  ba su tallafin kayayyakin abinci da sutura da sauransu. A bangaren gwamnati kuma mun sha aika masu da wasiku tare da gudanar da taron manema labarai inda, muna kira ga gwamnati ta cika alkawari da ta yi wa matan na biyan hakkin mazajensu don sun rasa rayukansu ne akan aiki. Saboda haka a matsayinmu na kungiya da ke kare hakkin wadannan matan ba mu zauna ba kuma bazamu zauna ba har sai an biya su hakkinsu kuma ga dukkan alama nan ba da jimawa ba za a yi hakan.
Aminiya: Wane irin nasarori kungiyarku ta samu?
Barista Hannatu: Alhamdulillah shekarata biyu kenan a shugabancin wannan kungiyar. Tun daga lokacin mun cimma nasarori da dama da suka hada da sulhunta matan Musulmi da inganta dangantaka tsakaninsu da wadanda ba Musulmi ba. Kuma muna gudanar da wa’azzuka inda muke gayyatan matan musulmi domin halarta karatuttuka da za su kawo masu canji mai ma’ana a rayuwansu.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kungiyarku ke fuskantar?
Barista Hannatu: A gaskiya akwai su da dama. Babbar matsalar ita ce ta rashin kudi. Kungiyarmu kamar yadda ka sani ba kungiyar gwamnati ba ce, kungiya ce mai zaman kanta. Kuma muna gudanar da ayyukanmu ne da kanmu. Kodayake a lokacin tsohon gwamnan jihar Nasarawa,  Abdullahi Adamu yana taimaka mana kwarai. Saboda haka nake so na yi amfani da wannan damar in yi kira ga duka matakan gwamnati da kuma jama’a masu hannu da shuni, da su taimaka mana musamman da kudi don mu samu damar gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata. Abu na biyu shi ne har yanzu ba mu iya kammala aikin sakatariyarmu ba. Wannan ma idan za a taimaka mana za mu yi maraba.
Aminiya: Ko kina da wani kira ga matan Musulmi?
Barista Hannatu: Kirana ga matan Musulmi da ma wadanda ba musulmi ba shi ne su tashi su nemi ilimi na boko da na addini don taimaka wa rayuwansu da ta ’ya’yansu. A kuma guje wa fadace-fadace a zauna lafiya da juna. Don dukanmu daya ne kuma Allah ya san dalilin da ya sa ya halicce mu tare.