✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin isassun ma’aikata na tarnaki ga asibitocin koyarwa – Dokta Alkali

Dokta Muhammad Alkali shi ne Babban Likitan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Asibitin ya yi bikin karrama ma’aikatansa da suka…

Dokta Muhammad Alkali shi ne Babban Likitan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Asibitin ya yi bikin karrama ma’aikatansa da suka nuna kwazo a ayyukansu, inda bayan an kammala bikin ya zanta da manema labarai:

 

Mene ne makasudin wannan taro?

Makasudin wannan taro shi ne mun san cewa muna da ma’aikata kuma mun lura cewa wannan asibiti na koyarwa da ke nan Bauchi ya kai sama da shekara tara da kafuwa, kuma mun yi la’akari da irin gagarumin ci gaban da muka samu da ba zai yiwu ba in ba da hadin kan ma’aikatan ba. Shi ya sa muka ce za mu yi wannan taro don godiya gare su baki daya, sannan a cikinsu muka dubi wadanda suka nuna kwazo a wadannan shekaru fiye da sauran muka ba su wasu kyaututtuka don kara nuna godiya gare su. Kuma mu asibiti ne da kowane mutum komai girmannsa cikin al’umma zai zo don mu duba lafiyarsa ko mu yi masa jinya. Kuma ka ga za mu iya samun bayani daga al’umma game da irin yadda mu’amalarmu da su take.

 

Wadanne matsaloli kuke fuskanta a nan?

Babban kalubalen da muke fuskanta wanda ya shafi yawancin tsarin da Gwamnatin Tarayya ke da shi ne na tafiya da ayyukan  hukumomin kiwon lafiya a kasar nan, wato batun karancin ma’aikata. Muna fama da karancin ma’aikata saboda wani tsari da gwamnati ta fito da shi na sanya takunkumin kan daukar ma’aikata, mu da muke aiki a asibitoci wannan babbar matsala ce gare mu don ta fi shafarmu. Ka ga da farko ba za mu iya kayyade yawan jama’ar da za su zo wajenmu neman magani ba, kuma a kowane asibiti za ka samu ana gina sababbin wurare amma an kasa bude su saboda rashin isassun ma’aikata. Kuma ya kamata a ware mu a ba mu wata kula ta musamman domin mu dauki ma’aikatan da suka dace don samun saukin gudanar da ayyukan jinya da kula da lafiyar al’umma. A wasu wurare muna da injuna sababbi na kula da lafiya amma ba mu da isassun ma’aikatan da za su kula da su, don haka muke rokon gwamnati ta cire wannan takunkumi. Don dukkan wuraren da muke kula da lafiya ko a ina ne za ka ga akwai karancin ma’aikata. Muna kara kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba wannan takunkumi na hana daukar ma’aikatun kula da lafiya domin a kauce wa hana mutane samun hanyar da za a kula da lafiyarsu. Ba za mu ce mara lafiya ya koma  gida ba, muna kan fadada cibiyoyin kula da lafiyar da muke da su, kuma idan ka fadada cibiyar kula da lafiya ba ka dauki ma’aikatan da za su yi maka aiki a wajen ba cibiyar ba za ta iya yin aiki ba. Ko a nan muna da cibiyoyi da mun kammala gina su amma saboda ba ma’aikatan da za su yi ayyukansu a wajen ba mu bude su ba.

 

Wannan asibiti ya kamata a ce yana kula da manyan cututtuka, amma sai ga shi har kananan cututtuka kuna kula da su ta yaya kuke tafiyar da wannan lamari?

Ka san a matsayinmu na asibiti ba za a kawo mana mara lafiya mu ce ya koma gida ba mu ba shi magani ba, ko ba za mu duba lafiyarsa ba. Duk da cewa mafi yawa daga cikin marasa lafiyar da suke zuwa suna zuwa da kananan cututtuka ko rashin lafiya ne amma muna da hakki a kanmu duk da cewa yawan marasa lafiya da ke zuwa ya kara mana yawaitar ayyuka, har ya kai ba mun mayar da hankulanmu kan manyan cututtuka ne kawai ba, amma duk da haka mun yi kokarin karfafa kanmu ta yadda za mu iya taka rawar da ake bukata wajen kula wa da manya da kananan cututtukan. Za mu yi kokari mu ci gaba da fadadawa amma dai a gaskiya yana shafan aikinmu kwarai da gaske.

 

Majinyata na kukan cewa kudaden da kuke karba a asibitin ya yi yawa ga talaka, me za ka ce?

Daga farko ba nufinmu ne mu rika karbar kudaden da mutane suke biya ba, amma a matsayinku na ’yan jarida ina so ku duba ku bincika ku ga kudin da muke karba a wannan asibiti da kudaden da wasu asibitocin koyarwa ke karba a kasar nan, za ku ga namu ne mafi sauki, saboda muna gudanar da wani tsari ne na kudaden maganin da kuka saya shi za mu sake sayo magani da su kuma mu yi wa wadansu jinya. Shi ya sa dole mu karbi ’yan kudade don samar da magunguna a asibitin ya dore. Duk da haka muna da wani tsari na kulawa da talaka wanda ba ya da halin da zai sayi magani a asibiti, akwai wani tsarin walwalar jama’a da muke da shi inda duk mutanen da muka bincika muka tabbatar da cewa ba su da halin biyan kudaden magani da jinya muna bin wani tsari na ganin  an yi musu jinya yadda ya kamata, kuma hukumar asibitin ce ke daukar nauyin biyan kudaden jinyar.

 

Wace shawara za ka bai wa ma’aikatan?

Babbar shawara da zan bai wa ma’aikata ita ce mu gane cewa muna aiki ne a inda ba mu isa mu rufe kofarmu ga kowa ba, kuma kowa zai iya zuwa wajenmu komai matsayinsa a cikin al’umma. Saboda haka kowa da irin zuwan da zai yi da irin halinsa. Ya kamata mu kara hakuri mu kara juriya da yanayin al’umma ta yadda zai zama kowa ya zo wurinmu mu yi hakuri da irin halinsa kuma mun biya masa bukata ba tare da mun samu matsala tsakaninmu da shi ba. Kuma mu dauki wadannan nasarori da muka samu cewa nasararmu ce baki daya saboda mun yi kokari ne baki daya, domin kowa da irin gudunmawar da ya bayar muka samu ci gaban da muka samu.