✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin biyan albashi yana barazanar durkusar da kasuwanci a Keffi’

An bayyana rashin biyan ma’aikatan Jihar Nasarawa albashinsu a matsayin abin da ke gurguntar da harkokin kasuwanci a babbar kasuwan garin Keffi da ke jihar.&nbsp…

An bayyana rashin biyan ma’aikatan Jihar Nasarawa albashinsu a matsayin abin da ke gurguntar da harkokin kasuwanci a babbar kasuwan garin Keffi da ke jihar.&nbsp

Shugaban Kasuwan Alhaji Rabo danbaba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilinmu game da harkokin kasuwanci a ofishinsa da ke kasuwar.
Ya ce a duk lokacin da ake samun matsalar rashin biya wa ma’aikatan jihar albashi ’yan kasuwan kan fuskanci matsaloli musamman na rashin samun ciniki da sauransu. Akan haka nema ya yi amfani da wannan damar inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi kokari ta biya ma’aikatanta don samun walwala a harkokin kasuwanci a kasuwar da sauran kasuwanni a jihar baki daya.
Da ya ke bayyani dangane da nasarori da ya cimma a matsayin shugaban kasuwar kawo hanzu Alhaji Rabo ya bayyana cewa a lokacinsa ne aka karbo naira miliyan 11 da Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-makura ya bai wa ‘yan kasuwar a matsayin tallafi a lokacin da gobara ta ci kasuwan kwanakin baya.
Ya kara da cewa a lokacinsa ne aka sanya manyan kofofi a manyan hanyoyin shiga kasuwar da kuma tabbatar an samu hadin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan kasuwar da dai sauransu. Ya kuma bayyana wasu daga cikin matsaloli da ’yan kasuwar ke fuskanta a halin yanzu da a cewarsa suka hada da “rashin tsabta a kasuwar.”
A karshe ya yi kira ga ’yan kasuwar da su ci gaba da hakuri da gwamnatin jihar don a cewarsa Gwamna Al-Makura mutum ne da ke son harkokin kasuwanci.