✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin aikin yi ya kai ni ga kera eriyar tashoshin talabijin -Usman Marafa

Usman Musa Marafa matashi ne, wanda ya kirkiri yin eriyar talabijin da ke kama dukkan tashohin Najeriya a Jihar Legas. Ya bayyana wa Aminiya cewa…

Usman Musa Marafa ke nan rike da samfurin eriyar da ya kirkiraUsman Musa Marafa matashi ne, wanda ya kirkiri yin eriyar talabijin da ke kama dukkan tashohin Najeriya a Jihar Legas. Ya bayyana wa Aminiya cewa iyayensa ’yan asalin garin Musawa ne a Jihar Katsina, amma an haife shi a Legas, inda ya yi firamare kuma ya fara karamar sakandare, daga bisani ya koma Jihar Katsina ya kammala a sakandaren dan Dattijo. Rashin kudi ya hana shi ci gaba, sai ya koma Legas domin ya nema ya koma karatu. Ga yadda sauran tattaunar ta gudana:
Ta yaya ka fara kera wannan eriya?
Na fara ne tare da wani abokina Mathew, kodayake tun ina karami nake gwada kere-kere. Bayan na kammala sakandare, kuma na rasa aikin yi, sai na yi tunanin kera eriya mai kama tashoshin talabijin a nan Jihar Legas. Bayan na yi nazarin yadda ake kera wasu eriyoyin, sai na fara kera tawa. Na fara da hada wayoyin da ke cikinta sannan daga bisani na kera ta wajen. A lokacin na sha wahala sosai, domin idan na kera ni da kaina nake fita na sayar da ita, kuma ga yadda Legas take da tsananin dokar hana tallace-tallace a kan titi, idan mutum ya yi arangama da jami’an hukumar kare muhalli.
Wane suna ka sanya wa eriyar?
Na sanya mata suna Eriya-’yar-Najeriya. Kuma idan ka lura za ka ga ta kunshi karfen aluminiyon da roba da kusoshi da waya da kuma salatif na leda. Na yi mata matattarar wuta, wacce take ba ta karfin kamo kowace irin tasha, kuma na yi  mata salo da kamanni yadda za ta ja hankalin mai saye. Sannan na sanya mata wurin da mutum zai sanya jikin talabijin dinsa don kamo tashoshin da yake so. Kuma tana da karfi sosai, yadda ba sai ka sayi eriya ’yar waje ba, ga saukin kudi. Domin eriya ’yar waje ta kai Naira dubu uku zuwa hudu, mu tamu ba ta wuce dubu daya. Na sami abubuwan a nan jihar Legas daga wurin masu sayar da kayan wutar lantarki.
Me ya sa ka kama kirkirar eriya a maimakon kasuwanci, kamar su harkar canji da mafi yawan matasa suke yi a nan?
Gaskiya a yanzu idan ka sami aiki za ka ga albashin ya yi karanci. Na lura albashi ba ya isar ma’aikata, ko kudin mota ba zai ishe ka ba. Kuma ni ba na sha’awar harkar canji. Na fi son kasuwancin da zan yi zaman kaina.
Wane buri kake so ka cimma a wannan sana’a?
Gaskiya ina so gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu ko kuma masu hannu da shuni su taimaka mini yadda zan fadada wannan fasaha ta yadda zan ci gaba da kera eriya da sauran kayan kere-kere. Allah Ya ba ni fasaha sosai. Idan na sami taimako, babu shakka zan taimaka wa jama’a. Zan bude babbar ma’aikata na dauki mutane aiki, har na rika fitar da kayayyakina kasashen wajen. Saboda haka ina so na yi amfani da wannan dama wajen sake rokon gwamnati, musamman ta Jihar Katsina da kuma ta Legas, su taimaka mini da jari.