✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin Adaidaita Sahu a manyan titunan Kano ya tilasta wa Kanawa tafiyar kasa

Matakin ya tilasta wa mutane da dama tafiyar kafa

Yayin da aka shiga rana ta farko da fara aiki da dokar hana baburan Adaidaita Sahu bin wasu manyan titunan birnin Kano, Aminiya ta lura cewa karancin ababen hawa ya tilasta wa dubban mutane tafiya a kasa.

Yayin da wasu kuma suka koma amfani da motocin daukar kaya kamar na kurkura da kanta, wasu kuwa tilas ta sa sun koma amfani da motocin Bas-bas da na Tasi da aka jima da yin watsi da su a cikin birnin.

A ranar Talata ce dai Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) ta sanar da hana baburan masu kafa uku bin wasu tituna a birnin, inda ta maye gurbinsu da dogayen motocin safa-safa da ta kawo.

Wasu fasinjoji a kan motar Kanta saboda rashin Adaidaita Sahu

Titunan da abin ya shafa sun hada da Ahmadu Bello Way da na Hadejia Road da kuma titin zuwa Gwarzo, tun daga shatele-talen Tal’udu.

Aminiya ta lura cewa an girke tarin jami’an tsaro da suka hada da na KAROTA da ’yan sanda da ma na sibil difens da ke hana babura bin wadannan titunan.

Mutane sun koma tafiyar kafa

To sai dai a zagayen da wakilan Aminiya suka yi a kan wadannan hanyoyin da safiyar Laraba, sun gane wa idanunsu yadda dubban mutanen da ba su da ababen hawa suna ta kokarin taka sayyada domin isa wuraren harkokinsu na yau da kullum.

Wasu fasinjoji a kan Kurkura

Sai dai kuma wakilan namu sun lura cewa babu isassun irin wadancan motocin da gwamnati ta samar a titin zuwa Gwarzo da na zuwa Hadejia, yayin da a na Ahmadu Bello Way kuwa, wakilinmu ya ce bai ga ko guda daya ba.

A maimakon haka, galibi mutane suka koma amfani da motocin Bas-bas da na Tasi, wadanda a baya Adaidaita Sahu ya kusa rabawa da sufurin cikin birni.

‘Gwamnati ba yi cikakken tanadi ba kafin sanya dokar’

A zantawarsa da Aminiya, wani da muka iske yana kokawar shiga motar Bas a kan titin zuwa Gwarzo, Abdullahi Bashir, ya ce shi dalibi ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma yanzu haka jarabawa yake yi, amma sai da ya shafe tsawon lokacin kafin ya sami motar Bas din.

Yadda mutane ke jiran abin hawa

Ya ce ba zai iya tuna yaushe rabonsa da hawa irin wannan motar ba sai yau, ita din kuma sai da kokawa.

“Sai da na yi tafiyar kafa sosai tun daga shatale-talen Tal’udu da Adaidaita Sahu ya ajiye ni kafin na samu Bas a kusa da marabar zuwa FCE, kuma a hakan ma da kokawa na samu shiga.

“Gaskiya bisa ga dukkan alamu gwamnati ba ta yi cikakken tanadi ba kafin fara sanya dokar, saboda wadannan motocin ba za su ishi fashinjojin da ke kan hanyar nan ba,” inji Abdullahi.

Ita kuwa wata da ta bayyana sunanta da Balaraba Kabiru, ta ce tana koyarwa ne a wani kauye da ke wajen Kano, kuma a matsayinta na matar aure da take zaune a cikin Kano, rashin babur din da zai fito da ita daga unguwarsu zuwa inda za ta sami mota zai iya sawa ta je aiki a makare.

“Yanzu alal misali, na haura minti 15 a nan ban sami abin hawa ba, ita kuma waccan doguwar motar ko da ta zo, tsaye-tsayenta ya yi yawa, ni kuma ina bukatar zuwa wajen aikina a kan lokaci.

“Ya kamata a samar mana mafita gaskiya, saboda muddin aka tafi a haka, zamu sha wahala,” inji ta.

A titin Ahmadu Bello kuwa, wanda ya fara daga kofar Gidan Gwamnatin Kano zuwa shatale-talen Mundubawa, wakilinmu ya ce bai ga ko da doguwar mota daya ba a can.

Hakan a cewarsa ya tilasta wa mutane na bin kowacce hanya domin nema wa kansu mafita, inda wasu ke hawa motar kurkura, babur mai kafa biyu, kanta yayin da wadanda ba za su iya jira ba suke tafiya a kafa.

Aminiya ta kuma ga wasu ’yan makaranta da suka ce tun daga makarantar Race Course Model suka tako a kafa zuwa Mundubawa saboda rashin abin hawa, duk da cewa wasu baburan na bin hanyoyin gefen titin.

Ko mara lafiya aka dauko a babur a kan wannan titin sai mun kama – KAROTA

To sai dai hukumar ta KAROTA ta bakin Shugabanta, Baffa Babba Dan-Agundi, ta ce babu gudu babu ja da baya a kan dokar hana baburan hawa wadannan titunan.

Shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi
Shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi

A cewar Dan-Agundi, duk babur din da suka gani a kan wadannan titunan, ko da mara lafiya ya dauko a kansa, jami’ansu za su kama shi.

Kazalika, ya ce dokar nan ta hana goyo a babur mai kafa biyu kowane iri ne ta dawo Kano, sannan akwai yiwuwar a fadada dokar hana Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan na Kano nan gaba kadan.